BindiddigiHoton matar da ake cewa na fuskantar shari’a kan...

Hoton matar da ake cewa na fuskantar shari’a kan ridda a Zamfara ba ita bace

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun asalin bidiyon hoton wacce akai ikirarin ita ce ke fuskantar shari’a kan ridda a jihar Zamfara wanda kuma Alkalanci ta ga no cewa wacce ke hoton da ake yadawa ita musulma ce wacce ta karbi musulunci a baya kuma ba a Najeriya ta ke zaune ba, tana kasar Amurka ne. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa hoton karya ne akai amfani da shi.
Shafin Sahara reporters ya fara wallafa labari da hoton wata budurwar inda shafin yace ita ce kw fuskantar shari’a a kotun musulunci kan ridda. amma daga baya ya goge hoton bayan awanni.
Hoton wanda Sahara reporters sukayi amfani dashi kafin Su goge
Wani shafin mai suna daily post ya wallafa labarin a ranar 20 ga watan Yunin 2025 inda ya bayyana cewa wata budurwa a Zamfara na fuskantar sharia a kotun musulunci saboda yin ridda zuwa addinin kirista. Shafin ya sanya hoton wata budurwa mai duhun fata a matsayin ita ce.
Hoton karya da Daily Post suka yada
Wani shafin ma mai suna intelregion shima ya wallafa wannan hoto da kuma labarin inda sh yace budurwa yar shekaru 22 mai suna Zainab Muhammadu na fuskantar hukuncin kisa saboda yin ridda.
Hoton karya da akai amfani da shi
Bincike:
Kafar tantance labarai ta gano wacce aka sanya hoton inda ta kasance daya daga cikin masu amfani da kafar sada zumunta wajen yin bidiyo da maganganu mai amfani da sunan Aalia Reeves. Shafinta na Instagram @aaliaa_reeves  shafin TikTok @Aaliareeves.
Hoton bidiyon da ta wallafa a shafin ta na Instagram
Bidiyon da aka dauki hoton dai ta wallafa shi a shafin ta na Instagram tana magana kan yadda take fama da mahaifiyarta tun bayan da ta karbi addinin musulunci.
Ta bayyana yadda a wasu lokuta mahaifiyarta wacce kirista ce take taimaka mata a wasu lokutan kuma take kin bata hadin kai. Ta kara da cewa ta sanya kawayenta da suka je Umrah da su sanya mahaifiyarta a addua.
Ita dai wacce akai amfani da hoton nata ba ma a Najeriya ta ke zaune ba. Tana kasar Amurka ne.
Gwamnatin jihar Zamfara ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar Sulaiman Bala Idris ta ce babu wata Zainab Muhammadu wacce ke fuskantar shari’a saboda ridda a jihar ta Zamfara.
Sakamakon bincike
:
Bisa samun asalin bidiyon hoton wacce akai ikirarin ita ce ke fuskantar shari’a kan ridda a jihar Zamfara wanda kuma Alkalanci ta ga no cewa wacce ke hoton da ake yadawa ita musulma ce wacce ta karbi musulunci a baya kuma ba a Najeriya ta ke zaune ba, tana kasar Amurka ne. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa hoton karya ne akai amfani da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Karanta wannan

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar