Hukunci: Ƙarya ne
Bisa sakamakon manhajar duba bidiyo da hotuna na cewa bidiyon hadin AI ne, da kuma kasa samun wannan bidiyo a shafin na Rarara wanda akai ikirarin cewa shine ya wallafa. Wannan ya sa Alkalanci yanke hukuncin cewa bidiyon da ikirarin karya ne.
Ikirari:
Akwai wani bidiyo da wani shafin Facebook mai suna Yaron Sokoto ya wallafa inda aka ga fitaccen mawakin nan Rarara da amaryarsa suna sumbatar juna tare da wata murya da ke ikirarin cewa; “wannan wani sabon bidiyo ne da Rarara ya saka shi a shafin sa yana…”
Wannan bidiyo dai ya sami mutane sama da miliyan daya da suka kalla yayin da sama da mutane dubu daya suka tofa albarkacin bakin su.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba shafin fitaccen mawakin Dauda Kahuta Rarara inda babu wannan bidiyo.
Haka zalika Alkalanci ta duba shafin amaryar ta Rarara wato Aisha Humaira amma babu irin wannan bidiyo.
Dauda Kahuta Rarara dai ya angwance da Aisha Humaira inda aka ga yadda ma’auratan suka gudanar da wata kasaitacciyar walima. ((https://www.facebook.com/share/p/18q1MCSaot/?))
Sannan Alkalanci ta yi amfani da manhajar duba hoto ko anyi amfani da kirkirarriyar basira ne inda ta samu sakamakon cewa bidiyo anyi amfani da AI ne wajen hadashi.
Sakamakon bincike: