Fayyace abubuwaWaɗanne ƙasashe ake ganin suna goyon bayan kafa gwamnatin...

Waɗanne ƙasashe ake ganin suna goyon bayan kafa gwamnatin ƴan tawaye a Sudan?

-

Ayyana gwamnatin ƴan tawaye da jagoran RSF Laftanar-Janar Mohamed Hamdan Dagalo ya yi a Sudan, ya zo a daidai lokacin da yaƙin basasar ƙasar ke cika shekara biyu, wanda ke nuna cewa yanzu kasar ta rabu gida biyu.

Ƙasashe da ake ganin suna goyon baya da kuma tattaunawa da gwamnatin ƴan adawa ta RSF sun hada da, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE da Kenya da Chadi da Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Habasha da kuma Uganda. Akwai kuma wani ɓangare na Sojojin Libya da suka ɓalle.

A lokacin da yake ayyana kafa gwamnatin adawa a ranar 15 ga watan Afrilu wannan shekarar, Laftanar-Janar Mohamed Hamdan Dagalo ya godewa Habasha da Chadi da Uganda da kuma Kenya. Birnin Nyala na yankin Darfur ne zai zama  fadar gwamnatin ta RSF da kungiyoyin kawance. Yawancin ƙungiyoyi da ke riƙe da makamai da kuma na siyasa sun yi yarjejeniya da RSF a watan Fabrairun bana, kan kafa gwamnatin da za ta fito daga yankunan Darfur da Kurdufan.

A watan Fabrairu, Al-Hadi Idris Yahya, babban jigon ƙungiyar Tasses ya yi iƙirarin cewa “suna da yakinin za su samu goyon baya daga ƙasashe da dama” kan kafa gwamnatin.

Ayyana gwamnatin ya ƙara janyo rarrabuwar kawuna a Sudan da kuma saka fargabar cewa ƙasar za ta faɗa cikin mawuyacin hali la’akari da halin gwamnatoci biyu da ake dasu a Libya.

RSF da ƙawancen ƙungiyoyi sun bayyana shirin fito da “sabuwar takardar kuɗi da kuma takardun zama ɗan ƙasa”, wanda masana ke ganin yunkurin ɓallewa ne.

Sai dai, Dagalo ya yi watsi da zargin neman ɓallewa daga Sudan. A maimakon haka, ya zargi gwamnatin sojin ƙasar da yin wasu abubuwa da za su kai ga rabewa, da kuma dawo da irin kuskuren da ya janyo ballewar Sudan ta Kudu.

Gwamnatin ƴan adawar za ta samar da sojoji da kuma ƴan sanda iri ɗaya, yayin da RSF da ƙungiyoyin ƙawance na ƴan bindiga za su kasance jigon dakarun.

Majalisar Ɗinkin Duniya, Ƙungiyar Tarayyar Afrika AU, Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa da Tarayyar Turai EU da kuma Amurka sun nuna adawa  da batun kafa gwamnatin ƴan tawaye da kuma nuna goyon baya ga haɗin-kan Sudan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Karanta wannan

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar