BindiddigiLabaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

-

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka haddasa wannan matsala ta kin jini, kyama da musgunawa tsakanin al’ummar arewacin Najeriya da kudanci dai abubuwa ne na labaran karya, yarfe da ake yadawa a kafafen sada zumunta dama maganganu a tsakanin al’ummar yankin.
Duk da cewa akwai matsaloli na zamantakewa tsakanin wasu al’ummar arewa da kudanci Najeriya to amma tun daga faruwar fadan siyasa da ya barke bayan sanar da sakamakon zaben shekarar 2011 wanda ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyin al’umma aka fara samin matsalar karuwar yaduwar labarun karya, wanda ya kai da wasu jaridu fassara karin maganar kare-jini-biri jini da tsohon shugaban kasa Buhari yayi da cewa jini zai malala da sauran fassara dai.
Wadannan labaran karya sun taimaka wajen kara kazantar alaka tsakanin mutanen yankunan biyu.
Haka zalika batun matsalar Boko Haram ta kara haddasa babbar matsala da kuma yaduwar labaran karya kan al’ummar arewa da su kansu na kudu.
A lokuta da dama ya kai matsayin da aka dauki duk wani dan arewancin Najeriya a matsayin dan ta’addan Boko Haram.
Wannan ya janyo kyara da tsana tsakanin al’ummar mutanen yankunan kasar biyu.
Cikin manyan labaran ƙarya da ake yaɗawa a tsakanin al’ummar wasu na nuna cewa ƴan arewa na goyon bayan ƴan fashin daji wato bandits misali wannan post a shekarar 2022 ((
Irin waɗannan labaran ƙarya dai sun haddasa cewa duk inda aka ga mafarauta a kudancin Najeriya ana ɗaukar su masu garkuwa da mutane ko ƴan ta’adda. Wannan ya janyo ƙona ƴan mafarauta goma shida a jihar Edo.
Wannan aika-aika ta bar baya da ƙura domin kuwa labarun ƙarya sun cigaba da yaɗuwa, yayin da a arewacin Najeriya wasu ka dinga yaɗa cewa ƙabilar Igbo ne suka aikata wannan kisa tare da wasu kalamai, alhali kuwa mutanen garin Uromi na jihar Edo ba Inyamirai bane wato ƙabilar su daban.
Sai kuma wasu ƴan Kudu da suka dinga yaɗa cewa tabbas waɗanda aka kashe masu garkuwa da mutane ne.
Haka zalika an sami yaɗuwar hotunan karyar harin ramakon gayya ga kabilun kudancin Najeriya a arewa.
Wasu ma sun yada wani bidiyon da akai amfani da kirkirarriyar basirar AI tare da cewa tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso yayi kira da ayi ramuwar gayya. Wanda Alkalanci ta gano cewa anyi amfani da bidiyon jawabin barka da Sallah da yayi ne wajen hada sautin karyar.
Haka zalika ana tsaka da wannan matsala wasu suka wallafa wani bidiyon ƙarya na cewa gwamnan jihar Edo ya bada umarnin rushe shuganan Hausawa.
Wato dai yaɗuwar labarai, hotuna da bidiyon ƙarya na cikin manyan abubuwan da suke haddasa ƙiyayya, asarar rayuka da duniyoyi tsakanin al’ummar yankunan Najeriya biyu wanda ya sanya idan ka ga ko kaji labari ka fara tabbatar da sahihancin da kafin ka aminta ko ma ka tofa albarkacin baki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Karanta wannan

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar