BindiddigiƘarya ne: Kamfanin Meta bai baiwa ƴan Najeriya wa'adin...

Ƙarya ne: Kamfanin Meta bai baiwa ƴan Najeriya wa’adin mako guda ba

-

Hukunci: Ƙarya ne
Binciken Alkalanci ya kasa samun wani waje da kamfanin Meta ya bayyana cewa ya ba ƴan Najeriya wa'adin mako guda kowa ya tabbatar da cewa sunan account ɗin sa yayi dai-dai da sunan katinsa na ɗan ƙasa ba. Sannan babu wani labari dake nuna cewa akwai haɗin gwiwa tsakanin Meta da gwamnatin Najeriya. Haka kuma babu inda Meta ya bayyana cewa yawan shafukan Facebook a Najeriya ya kai sama da miliyan 700. Bisa rashin samun sahihan bayanai daga a shafukan Meta da hukumomin gwamnatin Najeriya dangane da wannan iƙirarin yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ƙarya ne.
Hukumomi a Najeriya dai  sun rufe ko ace nome dubunnan shafukan sada zumunta bisa zargin su da laifuka daban-daban.
Iƙirari:
Wasu shafukan facebook dai sun wallafa iƙirarin cewa kamfanin Meta wanda ya mallaki Facebook, Instagram da Whatsapp ya baiwa ƴan Najeriya wa’adin mako guda kowa ya tabbatar da cewa sunan account ɗin sa yayi dai-dai da sunan katinsa na ɗan ƙasa ko wasu ID da aka aminta dasu.
Wani shafin na Facebook mai suna APA Hausa ya wallafa iƙirarin kamar haka;
Kamfanin Meta mamallakin shafukan sada zumunta na zamani mafiya girma a Duniya Facebook da Instagram, ya ba ƴan Najeriya wa’adin mako guda kowa ya tabbatar da cewa sunan account ɗin sa yayi dai-dai da sunan katinsa na ɗan ƙasa, saboda akwai adadin accounts fiye da miliyan 700 a Najeriya wanda kuma illahirin ƴan ƙasar basu wuce miliyan 230 ba, Meta yace zai rufe duk wani account ɗin bogi.”
Hoton labarin karya dake cigaba da yaduwa

https://www.facebook.com/share/p/1FAK9B5JXj/?mibextid=wwXIfr

Wani shafin ma mai suna Giade post ya wallafa wannan iƙirarin.
Hoton labarin karya dake cigaba da yaduwa
Bincike:
Binciken Alkalanci ya duba shafukan kamfanin na Meta amma babu wannan labari.
Haka zalika mun duba shafukan hukumomin gwamnatin Najeriya irin su NITDA da NCC to amma babu wannan labari.
To sai dai kafar tantance labarai ta Alkalanci ta ga bayanan dake nuna cewa Facebook ba ya bukatar sunan ka ya dace da na National ID, Fasfo, ko katin tuki ko katin zabe don amfani da shafin.
Amma  idan mutum yana son ayi verifying dinsa ko shafin mutum ya sami matsala (misali an rufe shi saboda taka doka), to za su bukaci ka tabbatar da kai ne mai shi ta hanyar ID.
Hakan dai na nufin ba dole bane sunan da ke Facebook ya yi dai-dai da na ID.
Haka zalika babu wata hadin gwiwa tsakanin Facebook da Gwamnatin Najeriya akan rufe shafuka.
Facebook kamfani ne mai zaman kansa. Ba ya aiki kai tsaye da gwamnati don rufe shafi sai idan akwai dalilan tsaro ko taka doka (kamar labaran karya, kutse, damfara, da sauransu).
Babu wata shaida dake nuna cewa Facebook ya goge ko nome miliyoyin shafuka saboda suna baiyi dai-dai da na ID ba.
Binciken Alkalanci ya gano cewa haka siddin Facebook ba zai goge shafin din mutum ba, dan kawai Username din ya banbanta da sunan dake a ID din mutum ba.
Yadda abun yake shine, idan mutum ya taka doka na Facebook, wanda ya haddasa rufe shafin,  duk lokacin da kazo ɗaukaka ƙara ko neman dawo da shafin da aka rufe zasu bukaci ID ɗinka wanda yayi daidai da sunan dake jikin shafin din naka. Idan baiyi daidai ba shine yake zama matsala duk da haka sukan warware matsalar a yawancin lokuta.
A tsarin kamfanin Meta zaku iya amfani da sunan da kowa ya fi saninku dashi, ko ma sunan banza, ko sunan sana’a. Wannan tsarin nasu yananan a rubuce a Facebook Help Center.
Sakamakon bincike: 
Binciken Alkalanci ya kasa samun wani waje da kamfanin Meta ya bayyana cewa  ya ba ƴan Najeriya wa’adin mako guda kowa ya tabbatar da cewa sunan account ɗin sa yayi dai-dai da sunan katinsa na ɗan ƙasa ba. Sannan babu wani labari dake nuna cewa akwai haɗin gwiwa tsakanin Meta da gwamnatin Najeriya. Sannan kuma babu inda Meta ya bayyana cewa yawan shafukan Facebook a Najeriya ya kai sama da miliyan 700. Bisa rashin samun sahihan bayanai daga a shafukan Meta da hukumomin gwamnatin Najeriya dangane da wannan iƙirarin yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ƙarya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar