A cikin watan Nuwamba, 2024, Hamdiyya Sidi, ’yar shekara 18 mazauniyar Jihar Sakkwato, ta wallafa wani bidiyo inda ta soki Gwamnan jihar ta Sakkwato, Ahmed Aliyu, saboda matsalolin tsaro da kuma cin zarafin mata a jihar. Inda ta buƙaci ’yan gudun hijira da su je ofishin Gwamnan a matsayin wata hanya ta nuna rashin jin daɗinsu da abubuwan da ke faruwa.
Bayan wannan wallafar ne, Rundunar ‘Yan Sandan jihar Sakkwato ta kama Hamdiyya kuma ta tsare ta, inda suka bayyana cewa kalamanta na iya tayar da tarzoma kuma ana tuhumar ta da laifin amfani da kalaman ɓatanci.
Sai dai bayan wasu watanni da faruwar wancan al’amari, an samu wallafe-wallafe da dama daga shafuka mabambanta a kafofin sada zumunta na Facebook da X wato twitter inda masu wallafar ke iƙirarin cewa kotu ta yanke wa Hamdiyya Sidi hukuncin shekara biyu a gidan yari tare da yi mata bulala 20.
Bayan zuzzurfan bincike da Alkalanci ta yi kan labarin, ta gano an fara wallafa shi ne tun a watan Afrilu, 2025 da harshen Turanci a kafar sada zumunci ta X (wato Twitter).

Bayan yi wa labarin na ƙarya kwalliya, wasu manyan shafuka da ke da dubban mabiya sun ci gaba da wallafa labarin da harshen Hausa.
Misali;
Sokoto News da ke da mabiya 1,300

Katsina News da ke da mabiya 13,000.

Daga fara yaɗa labarin dai zuwa yanzu an yaɗa shi sama da sau 370 daga mutane da shafuka daban daban a kafofin sada zumunta.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta tuntubi lauyan Hamdiyya Barista Abba Hikima inda ya bayyana wannan labari da cewa karya ne. Ya kara da bayyanawa Alkalanci cewa ya rasa me yasa ake kara yada wannan labarin karyar.
Haka zalika Alkalanci ta duba sahihan kafafen yada labarai amma ba a sami wannan labari ba.
Sannan Alkalanci ta duba yadda aka dinga cin karo na labari tsakanin shafukan da suka wallafa labarin.
Sakamakon Bincike:
Bisa ƙaryata wannan labari da lauyan Hamdiyya mai suna Barista Abba Hikima yayi da kuma kasa samun labarin a sahihan gidajen jaridu tare da samun rashin daidaito a shafukan da suka yada labarin yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin an yankewa Hamdiyya hukuncin shekaru 2 a matsayin labarin ƙarya.
