Kokarin zambatar mutane da yada labaran karya ta amfani da shafuka da kafofin sada zumunta da tura sako dai na cigaba da karuwa sosai.
Zamba ta yin amfani da kwaikwayo ko kamanni da shafuka na gaskiya, wanda ake kira phishing a turance, wani salo ne da wasu ke amfani da shafukan karya don samun ko satar bayanan mutane.
Wadannan shafuka na tambayar mutane su sanya bayanan su a shafin da yake kama da wanda yake na gaskiya.
Kwanakin baya kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta binciki tare da bankano shafin karya dake ikirarin yariman kasar Saudiyya zai kai mutane aikin hajji kyauta.
Haka zalika mun taba bincikar bayanin daukar masu jin Hausa a jihohin arewa da irin wadannan shafuka suna saka cewa majalisar dinkin duniya zata yi.
Na daya
Shafin na iya daukar bayanai dake kamanceceniya dana gaskiya to amma URL dinsa kan kasance ya sha banban. Yawanci mutane basa lura da URL face abunda aka rubuta.
Idan ka sami irin wannan sako kaje ka binciki shafin kamfanin ko kungiyar da aka ce na bada kyauta ko daukar aiki don samun bayani na gaskiya.
Wasu lokuta masu wannan aiki na yin sojan gona don zambatar mutane.
Idan kaga na wani babban mutum ne kamata yayi ka garzaya zuwa shafinsa na sada zumunta na gaskiya.
Na biyu
Ku dinga duba tsaron shafukan domin mafi yawancin lokuta shafuka na gaskiya na amfani da tsaro wajen ayyukan su. Da zarar ance shafi bashi da tsaro to akwai alamar tambaya a kansa.
Yadda zaku gane shafi mai tsaro da maras tsaro shine.
A saman shafin inda ake shiga zaku ga HTPP da zarar baku ga S a karshe be wato https to bashi da tsaro mai S shine mai tsaro.
Masu sojan gona da yan zamba na zuwa da shafuka dake kama dana gaskiya don haka ku dinga lura sosai kan shafukan da zaku dinga shiga Idan an turo muku.
Yanzu ana samin shafukan zamba masu dauke da S don haka ku duba na kasa don ganin yadda zakuyi.

Na uku
Idan kuna da tantama zaku iya tantance shafi kafin ku shiga cikin sa. Akwai hanya kyauta da zaku iya bi don tantance shafi. Misali https://whois.domaintools.com/ domin duba bayanan shafin.
Na hudu
Ku gudu duk wani shafi ko sako da za’a ce ki turawa mutum goma. Ko kuma sakon da za’a ce kuyi ta turawa sai yakai wani adadi kafin ku sami damar shiga shafin.
Ga misalin irin wadannan shafuka na sojan gona da zamba cikin aminci: