BindiddigiKasashe KetareYadda wasu ƙasashen Larabawa, Rasha, Amurka suka dinga taimakawa...

Yadda wasu ƙasashen Larabawa, Rasha, Amurka suka dinga taimakawa Isra’ila yayin yaƙin Gaza

-

Aƙalla ƙasashe sama da sittin ne sabon rahoton Majalisar ɗinkin duniya ya nuna cewa sun taimakawa ƙasar Isra’ila yayin da take kai hare-hare a Gaza wanda yayi sanadiyar mutuwar dubban Falasɗinawa. Duk da cewa rahoton ya nuna yadda wasu suka janye goyon baya ko taimakon da suke bayarwa saboda da yadda yakin ya sauya salo.

Rahoton da mai rahoto ta musamman ta MDD Francesca Albanese  ta fitar ya nuna kashe-kashen da ya faru a Gaza ya sami tallafin wasu manyan ƙasashen duniya.

Francesca Albanese mai rahoto ta musamman na Majalisar Dinkin Duniya

Rahoton ya bayyana cewa abu ne mai wuya ace Isra’ila ta iya aikata kisan kiyashin Gaza ba tare da taimakon manyan ƙasashe ba, musamman ta hanyar ƙarfafa kasuwanci, bada makamai da sauran su.

Taimakon ya haɗa da na kai tsaye, kayan aiki, kariya ta diflomasiya, wasu ma harda tura soji da kayan yaƙi.

Albanese wacce zata gabatar da rahoton daga ƙasar Afrika ta Kudu saboda tuntuni Amurka ta sanya mata takunkumi.

Ƙasashen Larabawa 

Abun mamakin shine yadda rahoton ya bankaɗo yadda wasu ƙasashen Larabawa na da hannu wajen taimakawa Isra’ila yayin hare-haren Gaza.

Ƙasashen sun haɗa da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE, Jordan, Qatar, Masar (Egypt) da Maroko. Waɗannan ƙasashe sun ƙarfafa kasuwanci da ƙasar Isra’ila tun daga watan Oktoban shekarar 2023.

Afrika ta Kudu

Duk da cewa ƙasar Afrika ta Kudu ita ce kan gaba na ƙarar Isra’ila a kotun hukunta manyan laifuka ICC, kan tuhumar Isra’ila da kisan kiyashin, to amma rahoton ya sami ƙasar da baiwa Isra’ila kayan haɗa makamai.

Ƙasashen Yamma

Rahoton dai ya bayyana ƙasashen Amurka, Rasha, Jamus da Italiya a matsayin waɗanda suka zama jigo wajen tallafawa Isra’ila wajen yaƙin Gaza.

Ita kuma ƙasar Birtaniya ta taimakawa Isra’ila da bayanai domin tayi amfani da jiragen samun bayanai wato surveillance flights sama da 600  daga sansanin ta dake Cyprus cikin lokutan da Isra’ila ta ɗauka tana kai hare-hare a Gaza.

Manyan ƙasashen da suka taimakawa Isra’ila da man fetur yayin kisan kiyashin Gaza

Akwai ƙasashen da suka cigaba da alaƙa ta kusa da Isra’ila tare da kai musu kayayyaki iri-iri wanda ya haɗa da makamai. Ƙasashen dai sune Amurka da Rasha sai kuma ƙasashen Brazil, Kazakistan da Turkiyya.

Tallafin bangaren jiragen yaki

Rahoton ya kuma ware ƙasashe 12 da suka baiwa Isra’ila tallafin ɓangare na jirgin yaƙi ƙirar F-35 jets.

Ƙasashen sun haɗa da Amurka, Birtaniya, Kanada, Jamus, Austaraliya.

Ƙasashen da suka ɗauki matakin daina sayar da makamai wa Isra’ila 

Wasu cikin waɗancan ƙasashe sun sanya wa Isra’ila takunkumin sayar da makamai saboda kisan Falasɗinawa.

Ƙasashen sune; Spain, Belgium, Kanada, Japan, Italiya, Slovania da The Netherlands

Ƙasashen da suka sanya takunkumi wa wasu jami’an Isra’ila 

Daga shekarar 2024 wasu daga cikin ƙasashen dake taimakawa Isra’ila sun sanyawa wasu jami’an Isra’ila da suka bayyana a matsayin masu tsattsauran ra’ayi.

Ƙasanshen sun haɗa da; Ƙungiyar Tarayyar Turai EU, Kanada, Birtaniya da Norway

Ƙasashen da suka daina alaƙa da Isra’ila tun shekarar 2023

Rahoton na majalisar ɗinkin Duniya dai ya bayyana ƙasashen Belize, Bolivia, Colombia da Nicaragua.

Ƙasashen da suka rage alaƙa da Isra’ila 

Sai kuma ƙasashen da suka rage ƙarfin alaƙa da Isra’ila sun haɗa da; Bahrain, Chadi, Chile, Hondarus, Jordan, Turkiyya da Afrika ta Kudu.

 Ƙasashen da ƴan ƙasarsu ke cikin sojin Isra’ila 

Tun daga shekarar 2023 akwai sojoji daga ƙasashe waje dake aiki tare da sojin Isra’ila wajen yaƙi a Gaza. Ƴan waɗannan ƙasashe dai sun haɗa da; Rasha, Amurka, da Birtaniya

Rahoton dai ya ambato ƙasashe da dama da suka taimakawa Isra’ila.a fannoni da dama

Indiya, Austaraliya, Amurka, Kanada, Italiya, The Netherlands, Girka (Greece), Serbia, Denmark, Poland, Birtaniya, Belgium, Finland, Jamus, Czech Republic, Koriya ta Kudu, Singapore da Switzerland

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar