Abun lura dangane da wannan scholarship da ake tallatawa yanzu haka shine ta yaya mutum zai iya tafiya wata ƙasa ba tare sa Fasfo ba kuma karatu daga matakin digiri na farko har zuwa na uku.
Sannan baya ga cewa karatu kyauta kuma akwai ɗan na kashewa da za’a dinga bawa mutum, tallan wannan scholarship ya ƙara da kwaɗaitar da mutane cewa zasu iya aikin da zasu sami kuɗi sama da kuɗin da ya kai Naira N1,000,000.
Sannan an rubuta cewa mutum na da damar zama ɗan Rasha Idan ya cike wasu sharuɗɗa.
Waɗannan batutuwa dai sunyi kama da irin yaudarar da akawa da dama daga ‘yan Afrika wajen shiga yaƙi ko kuma bautar dasu wajen ƙera jirage marasa matuƙa.
Me hukumomi ke cewa?
Jakadan ƙasar Ukraine a Najeriya Ivan Kholostenko ya shawarci ‘yan Afrika da su kula matuyka dangane da scholarship daga ƙasar Rasha musamman kasancewar sojin Ukraine sun sha kama ‘yan Afrika da Rasha ke amfani dasu a matsayin sojoji.
“Bayanan da muke da su sune Rasha na amfani da ‘yan kasashen waje wajen yaƙi da ƙasar mu, tana saka su cikin haɗari domin cimma burinta. Ya zuwa yanzu akwai ‘yan Afrika da dama dake gidajen yarin Fursunonin yaƙi bayan da Rasha ta tura su fagen yaƙi.”
Shima Jakadan ƙasar Rasha a Najeriya ya musanta zarge-zargen amfani da scholarship na bogi.
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya dai ta jaddada bukatar ‘yan Najeriya su yi taka tsan-tsan wajen cike ko karɓar guraben karatu kyauta wato scholarship saboda akwai na bogi ko yaudara dake bautar da mutane ko safarar su.