Akwai dai iƙirarai kala-kala kan batun ƙarfin namiji a gado da kuma tsawon lokacin daya kamata ya ɗauka yana jima’i wanda zai tabbatar da cewa lafiyar sa ƙalau.
Akwai masu sayar da magunguna kala-kala a kasuwanni, masallatan juma’a, layuka daban-daban dake iƙirarin cewa suna ƙara ƙarfin namiji ne a gado wato yayin jima’i. Wasu na sirrantawa wasu kuma na faɗar abin kai tsaye wanda hakan a al’adar Bahaushe batsa ne da rashin ta ido wato kunya.
Labarin mutuwar mazaje ta sanadiyyar shan maganin ƙara ƙarfi ko kuzari domin yin jima’i ba sabon abu bane
Akwai irin wannan misalai da dama wanda likitoci da jami’an ƴan sanda suka tabbatar.
Hukumar kula da abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC tasha kiran ‘yan Najeriya dasu guji shan magungunan kara karfin maza.
Akwai wani lokaci da saura ƙiris a yi wa wani tiyatar kashe mazakutarsa bayan ta ƙi kwantawa na tsawon kwanaki bayan da ya sha maganin ƙara ƙarfin gaba.
Menene ɗaukewar sha’awar ɗa namiji erectile dysfunction?
Wannan matsala ce ta gaban ɗa namiji dake addabar miliyoyin mazaje a faɗin duniya.
A ƙalla dai sama da maza miliyan 300 ne ke fama da wannan matsalar ta ɗaukewar sha’awa da rashin tashin gaba tare da ka sa yin jima’i yadda ya kamata da ake kira erectile dysfunction.
Bincike ya nuna cewa a wasu ƙasashen Afrika kashi 30 na maza na fama da wannan matsala.
Erectile dysfunction shine daukewar sha’awa, rashi ko wahalar tashin gaba da samun yin jima’i.
Wannan matsala ce da ke fuskantar majaze na kowanne shekaru amma dai yafi shafar masu shekaru da dama a cewar masana harkokin lafiyar mafitsara.
Abinda ke janyo matsalar gaban namiji
Abubuwan dake haddasa wannan matsala sun kasu kashi biyu a cewar Dr. Bello Abdulhakim likita dake aiki a asibitin ƙasa a Abuja Najeriya.
Kashi na farko
Matsalar dake da alaƙa da halayya wato psychological, da kuma fannin tattalin arzikin mutum.
Dr. Bello yace idan mutum na fama da matsalar karyewar arziki, rashin kuɗi, kora daga gurin aiki da makamantansu hakan na iya janyo daukewar sha’awa da rashin tashin gaba da kasa yin jima’i.
Kashi na biyu
Matsalar dake alaƙa da lafiyar jiki
Kansar mafitsarar namiji ta prostrate
Ciwon suga na type 2
Hawan jini
Cutar ƙwaƙwalwa
Ciwukan masu tsanani na rashin bacci ko yin bacci sosai
Kwayoyi misali na hawan jini, ciwon suga da sauran su
Cutar damuwa da sauran ciwuwwuka da zaku iya karantawa a nan.
Menene kawowa da wuri wato premature ejaculation?
Shi kuma wannan shine da dama ake ɗauka a matsayin babbar matsala.
Babu dai wani cikakken bincike da yake nuna ummul aba’isin kawowa da wuri da maza keyi lokacin jima’i, duk da cewa suna da alaƙa da yanayin da namijin ke ciki na;
Tsoron kada ya gaza
Alaƙa da wacce yake saduwa da
Halin da yake ciki
Da sauran su
Mintina biyu kaɗai a jima’i rashin lafiya ne?
Mun tambayi Dr. Bello Abdulhakim inda yace iƙiraran da ke yaɗuwa a tsakanin al’umma kan lokutan da sai mutum ya ɗauka yana jima’i galibi ƙarya ne.
“Misali zakaji masu sai da maganin a tituna ko kasuwanni na cewa sai mutum yayi awa kaza ko kaza sannan ya cika namiji.”
Ya kara da cewa; “Zaka ji suna cewa yin mintuna biyu a jima’i kaɗai rashin lafiya ne.”
Dr. Bello yace; “gaban namiji na iya tashi kuma ya kasa shiga farjin mace wato penetration, wannan matsala ce, Sannan yana iya ya kasa tashi kwata-kwata. Abinda mutane basu sani ba shine mu a wannan fanni indai mutum yayi mintuna biyu yana jima’i to tabbas lafiyar sa ƙalau ta fannin jima’i sai dai ko idan yana da wata rashin lafiyar da ban.
Mutane da dama basa lura da yanayin rayuwa da lafiyar su da zasu iya gano cewa tashin gaba, ɗaukewar sha’awar da ta zo musu me ya janyo ta? Wata damuwa ce, rashin kuɗi ne, ko wani magani da suke sha ne? Mutane basa duba wannan sai ko dai suje waje su gwada da matan banza ko kuma susha ko dai magungunan gargajiya ko ma na bature don ƙara musu ƙarfi.”
Wani bayani da aka wallafa a wata mujalla ya nuna cewa duk saduwar da namiji ya kawo ƙasa da minti ɗaya da sakan talatin hakan na nuna akwai matsala da ake kira premature ejaculation.
Akasarin maza masu fama da matsalar rashin ƙarfin gaba su na boye halin da suke ciki.
Wasu daga cikin dalilan da ke sakawa maza ba sa iya fitowa su bayyana sun hada da al’adar jin kunya da ke tattare da batun a cikin al’umma, wanda ke iya haddasa su fuskanci tsangwama, da rashin ganin kima da kuma tsegumi idan suka fito suka fada wa abokan zamansu ko kuma wasu mutane daban.
Sakamakon haka, su kan riƙa fama da wannan matsala a boye.
Hakan kuma na ƙara sa matsalar gaban nasu ya ƙara ta’azzara, saboda maza masu fama da irin wannan matsala kan fara jin tsoro har ma da ƙauracewa duk wata mu’amala da ta shafi yin jima’i.
