Fayyace abubuwaYadda aka yaudari ‘ƴan Afrika shiga yakin Rasha da...

Yadda aka yaudari ‘ƴan Afrika shiga yakin Rasha da Ukraine

-

 

Tun da Rasha ta fara mamaya a kasar Ukraine a shekarar 2014 ake cigaba da rasa rayukan sojoji da fararen hula tsakanin kasashen biyu.
Babbar mamayar da Rashan taso yi a Ukraine ta girmama a shekarar 2022 wanda kasar ta Rasha ta kai hare-hare har kusa da Kyiv babban birnin kasar Ukraine.
An sha zargin Rasha da yaudarar ‘yan Afrika tare sa tura su fagen yaki ko kera makamai ta hanyar amfani da cewa za’a basu tallafin karatu ko aikin yi.
Gidan yarin fursunonin yaki
Daya daga cikin abinda ya ja hankali na a ziyarar kasar Ukraine da nayi shine, na yadda aka sami ‘yan Afrika takwas a cikin gidan yarin Ukraine wadanda suke fursunonin yaki wato sojojin Rasha da aka kamo a raye.
An bamu damar shiga wannan gidan yari wanda ke dauke da fursunonin yaki sama da dubu daya, wanda ya hada da asalin yan kasar Rasha da kuma wasu daga kasashen Asiya da Latin Amurka.
Wasu daga cikin fursunonin yaki
Yayin ganawa da wani dan kasar Sri lanka wanda ya bayyana cewa neman samun Fasfo din Rasha ne yasa ya shiga aikin sojin Rasha domin yaki da Ukraine.
Ganawa da fursunan yaki dan kasar Sri Lanka
Ya ce an masa alkawarin Idan har ya shiga soji kuma yayi yaki na shekara daya za’a bashi Fasfo din kasar Rasha.
Fursunonin yaki ‘yan Afrika
A ganawa da fursunonin yaki daga Afrika wani dan kasar Ghana mai suna Joshua ya ce ya je Rasha ne domin samun tallafin karatu wato scholarship wanda daya je sai ya tarar ba abinda ya gani a yanar gizo bane. Ya kara da cewa a wannan yanayi ne wasu ‘yan Najeriya suka sameshi kan akwai wata yarjejeniya da Idan ya sanya hannu zai sami kudin da zai biya kudin karatun sa dama sauran bukatu.
Bayan ya sanya hannu ne dai ya gane cewa zuwa fagen yaki ne. Ya ce ba tare da bashi wani horo da ya kai sati daya ba aka bashi khakin soja da binda ya tafi fagen yaki da kasar Ukraine.
Kwana daya da fara yakin ne aka kai hari a tawagar da yake inda suka tarwatse, ya dinga tafiya bai san inda zashi ba anan ne sojojin kasar Ukraine suka kama shi.
Ya bayyana cewa ya bar matarsa a Dubai dauke da cikin wata biyar a lokacin da ya tafi Rasha. Ya ce “yanzu haka nasan iyaye na, ‘yan uwa na na can na tambayar matata cewa Ina mijinta, Idan uban danki? Ina nadamar daukar wannan mataki.”
Fursunan yaki dan kasar Ghana
Dan Somalia
Shi kuwa Adil Abdallah ya ce ya sami bizar zuwa Rasha a Nairobi. Ya ce ya bar kasar sa ne saboda neman kudi da kuma Fasfo din Rasha. Ya ce kasar sa ba ta da arziki kuma Fasfo din kasar bashi da karfi.
Ya fara da kananan ayyuka inda daga nan ne aka kwadaita mishi cewa Idan ya shiga soja za’a biya shi dala dubu ashirin da kuma dala dubu biyu duk wata da kuma samun Fasfo din Rasha.
Ya ce babu wani horo da aka bashi kafin a tura shi fagen fama. Ya kara da cewa kwana hudu da zuwa fagen fama aka kama shi.
“Yanzu na kai sama da shekara guda a nan, sau daya na taba magana da iyayena tunda na shigo nan.”
Cikin bayanin sa Adil ya tsani yadda kasar sa take cikin talauci wanda yasa har ya sanya hannu a yarjejeniyar.
Dan Egypt
Akwai ‘yan kasar Egypt guda hudu, daya daga cikin wanda muka tattauna da ya bayyana cewa shi karatu ya kawo shi Mascow, to sai dai ya shiga shaye-shaye da sayar da kwayoyi wanda aka kamashi aka yanke masa shekaru bakwai a gidan yari.
Ya bayyana cewa a cikin yarin ne aka ce Idan ya amince ya shiga soji kuma yayi yaki na shekara daya za’a yafe masa laifin daya aikata.
Fursunan yaki dan kasar Egypt
Ya bayyana cewa ya amince ne domin ya sami ‘yanci.
Akwai sauran ‘yan Afrika a cikin gidan yarin daya daga Togo, daya daga Mali. Daya daga Ghana, daya daga Mali, daya daga Togo, sai hudu daga Egypt da kuma daya daga Somalia.
Fursunonin yaki ‘yan Afrika
Musayar Fursononi 
Rasha da Ukraine dai na musayar fursononin yaki akai-akai.

To amma yayin wannan musaya an taba yi da ‘yan Afrika ko wasu kasashe ba yan asalin Rasha ba? Tambayar da mukayi yiwa dukkan Afrikan dama wadanda suke masu duhun fata. Sun bayyana cewa tunda ake musayar fursononin yaki ba’a taba yi da ‘yan Afrika ko wasu da suka kasance ba asalin kasar Rasha ba.

Fursunonin yaki
Sai dai wani jami’i a hukumar leken asiri ta kasar Ukraine ya bayyana cewa suna kokarin tuntubar kasashen da wadannan fursononin yaki da aka yaudara suka futo domin ganin an maida su kasashen su na asali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta TikTok wanda ke nuna cewa jami'an tsaro sun kwashe...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Karanta wannan

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar