Yaƙin Sudan dai ana yin sane tsakanin dakarun sojin ƙasar wanda Janar Abdul Fatah Al-Burhan ke shugabanta kuma shine shugaban ƙasa da dakarun RSF da Janar Mohammed Hamdan Dagalo ke shugabanta.
Su dai dakarun RSF an samar dasu ne a shekarar 2013, wanda à baya suka kasance cikin ƙungiyar janjaweed da sukai yaƙi a yankin Darfur kuma ake zargi da kisan ƙare dangi a shekarar 2003.
Tun daga wancan lokaci dai Janar Dagalo ya samar da dakarun da ake amfani da su wajen yaƙi a ƙasashen Libya da Yemen.
Janar Dagalo ya buƙaci a haɗe dakarun RSF da sojojin ƙasar tare da basu ikon jagorancin soji, haka zalika ya bukaci ya kasance mai kula da ma’adanin zinaren ƙasar.
Ƙasashen Amurka, Burtaniya, Majalisar Dinkin Duniya da Ƙungiyar human rights watch sun zargi RSF da kisan ƙabilanci wato kashe ƙabilun da ba larabawa ba, da baƙaƙen fata.
Duk da cewa ƙungiyoyi irin su Amnesty sun koka kan yadda ƙasashen duniya sukai shakulatin ɓangaro da yaƙin Sudan, to amma shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron a bara ya ayyana taimakon Euro biliyan biyu domin tallafawa waɗanda wannan yaƙi ya shafa a Sudan.
Ƙasashen dake rura wutar yaƙin:
ƙasashen Libya, Chad da Sudan ta Kudu ne dai wani jami’in majalissar ɗinkin duniya ke zargi a matsayin masu rura wutar tun farkon yaƙin har zuwa yanzu, a cewar jaridar dillancin labarai ta Reuters.
Ƙasashen Burtaniya da Amurka kuwa sun zargi kasar haɗaɗɗiyar daular Larabawa UAE da cewa itace ke baiwa RSF makamai, wanda ƙasar ta musanta.
Har ila yau ana zargin ƙasar Saudiyya da hannu wajen goyon bayan RSF kasancewar dakarun RSF ne ƙasar ta Saudiyya ke amfani wajen yaƙi a ƙasar Yemen.
A baya-bayan nan kuma an gano ƙasar Kenya wanda shugaban ƙasar ya karbi tare da amincewa da dakarun RSF wajen kafa shugabanci a ƙasar Sudan wanda ƙasashen duniya da dama sukai Allah wadai da matakin na Kenya.
Wani ɗan jaridar ƙasar Kenya ya bayyanawa Alkalanci cewa dalilin da yasa shugaban Kenya Ruto ke goyon bayan mayaƙan RSF shine shugabannin mayaƙan abokan kasuwancin sa ne da daɗewa.
A ƴan kwanakin da suka gabata ne dai dakarun sojin ƙasar ta Sudan suka kwace fadar shugaban kasa da babban birnin ƙasar Khartoum daga hannun RSF.
Labarai Masu Alaka: