Shekarar 2025 dai ta kasance shekarar da aka sami wasu shafukan sada zumunta da kaso mafi yawa na abubuwan da suke wallafawa kan kasance na ƙage, ƙarya ko kuma ƙarin gishiri wato zuzuta labari.
Yayin da mutane kan karanta labarai, kallon bidiyo da hotuna ta kafafen sada zumunta, buƙatar tantance labarai ko bidiyo da hotuna na cigaba da ƙaruwa domin yadda wasu shafukan ke yaudarar masu karatu ko kallo.
Akwai dai wasu abubuwa dake faruwa da suke haddasa wallafa ƙage da labaran ƙaryar, yayin da wasu kuma tsofaffin labarai, hotuna ko bidiyo ake dawo dasu domin yaudarar mutane.
A nan zamu kawo muku wasu daga cikin shafukan dake yaɗa labaran ƙarya wanda Alkalanci ta bi diddigi na tsawon lokaci.
Wakiliya
Wannan wani shafin Facebook ne mai suna Wakiliya wanda ke da mabiya sama da dubu ɗari biyu da arba’in da biyu (242k).
Shafin ya wallafa wani labarin dake cewa maciji ya haɗiye kuɗi a kamfanin mai na NNPCL sama da naira tiriliyan ɗari biyu da goma (₦210tr).
Wannan labari dai ya kasance na ƙarya.
Shafin ya wallafa wani labarin inda yake cewa limamin babban masallacin ƙasa Farfesa Maƙari ya zama malamin daya fi kowanne ilimin hadisi a Afrika. A watan Augusta ma shafin na wakiliya ya wallafa wannan labari inda ya sami comments sama da dubu biyu. A watannin baya Alkalanci ta tantance wannan labari inda da kansa Farfesa Maƙari ya musanta wannan labari.
Shafin na Wakiliya ya wallafa wani labarin dake cewa shugaban ƙasar Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore ya ayyana haramcin shan giya.
To sai ƙasar ta Burkina Faso kasancewar ƙasa mai mutane mabiya addinai da kuma al’adu hakan abu ne mai matuƙar wuya. Haka zalika babu wannan labari a kafafen yaɗa labaran ƙarya, inda wani ɗan ƙasar ya ƙaryata wannan labari.
Burkina Faso hana shan giya
Shafin ya wallafa labarin cewa mutane sama da dubu ɗari takwas (800k) suka bar ɗarika a karatun Shaikh Guruntum.
Sai dai babu inda Shaikh Guruntum ya gudanar da karatu aka sami irin wannan adadi na halarta balle ace waɗanda suka bar wata ɗarika sun kai wannan wa’adi.
Alfijir News
Shima wannan shafin na Facebook mai mabiya sama da dubu ɗari biyu da sittin da daya (261k)
Shima wannan shafin Facebook na Alfijir News ya wallafa labaran ƙarya sosai a shekarar 2025.
Ya wallafa labaran ƙarya makamancin wanda shafin Wakiliya ya wallafa. Batun haɗiye a NNPCL da na labarin Farfesa Maƙari a matsayin wanda yafi koma ilimin hadisi a Afrika. Dukkan wadannan labaran karya ne.
Sannan shafin ya rawaito labarin ayyana Shaikh Shareef Saleh a matsayin wanda aka naɗa shugaban Tijjaniyya. Duk da cewa an jiyo babban ɗan Shaikh Dahiru Usman Bauchi yana bayyana mubaya’arsa da cewa zasu goyi bayan shugabancin Shaikh Shareef Saleh, to sai dai ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan labari ba a sami wata takardar naɗi daga Khaulaha ba, ina daga can ne dama ake naɗin shugabancin Tijjaniyya.
Ana dai samun ƙaruwar shafukan dake yaɗa labaran ƙarya a kafafen sada zumunta.
Kusan dukkan shafukan dake yaɗa labaran ƙarya basu da shafi wato website na musamman da suke wallafa labaran su. Cikin wadanda Alkalanci ta fahimci na yada labaran karya lokaci zuwa lokaci sun hada da shafin Facebook mai suna Qugiya Hausa.
Waɗannan shafuka ne dake wallafa labaran su a kafafen sada zumunta suna iƙirarin kasancewa gidajen jaridu da mutane zasu aminta dasu wajen kawo musu sahihan labarai.
