Bisa kasa samun wadannan a gidajen jaridun ƙasar Nijar da Burkina Faso da kuma bayanin jami'in ma'aikatar harkokin wajen ta Nijar da ya tabbatar wa Alkalanci cewa wannan labari ba gaskiya bane, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin ƙarye ne.
A duk lokacin da aka sami wasu manyan bayanai musamman tsakanin ƙasa da ƙasa ko wasu jigogin siyasa, wasu kan yaɗa labaran ƙarya domin cimma manufa.
Iƙirari:
Akwai wani iƙirari dake yaɗuwa a kafafen sada zumunta ina ake iƙirarin cewa shugaban Nijar yace ya sha alwashin harbo makamin da Amurka zata harba zuwa Najeriya.
“Shugaban mulkin soji na kasar Nijar Janar Muhammad Tchiani ya bayyana cewar ku barta ta harbo, babu wani màkàmìñ daya isa ya gitta ta sararin samaniyar kasar Nijar ba tare da mun kàkkàɓo shi ba, kuma a shirye muke da mu tsunduma cikin yà+ƙì gadan gadan da Amurka matuƙar tayi gigin kaiwa ƴan uwanmu na Najeriya hà+rì.”
Duk da girman wannan bayani dai gidan jaridar ƙasar bai rawaito labari makamancin hakan ba. Haka zalika jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Nijar ya faɗawa Alakalanci cewa ya zuwa yanzu babu wani bayani da gwamnatin Nijar ta fitar dangane da abinda ke faruwa tsakanin Nijar da Amurka.
Sakamakon bincike:
Bisa kasa samun wannan labari a gidajen jaridun ƙasar Nijar da kuma bayanin jami’in ma’aikatar harkokin wajen ta Nijar da ya tabbatar wa Alkalanci cewa wannan labari ba gaskiya bane, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin ƙarye ne.
Shugaban Burkina Faso
Iƙirari:
Akwai wasu shafukan da suka yaɗa cewa shugaban Burkina Faso Ibrahim Traore ya gargaɗi Amurka da kada ta kaiwa Najeriya hari.
Wannan shafin na Facebook har sanya murya yayi a matsayin rahoto tare da yada ikirarin cewa shugaban Burkina Faso yayi magana kan wannan batu na Najeriya da Amurka.
Labarin karya dake yaduwa
Shi kuma wannan shafin na Facebook cewa yayi shugaban na Burkina Faso ya gargadi shugaban Amurka Trump kan Najeriya.
Labarin karya dake yaduwa
Bincike:
Shi ma wannan labarin duk da girman sa babu wata sahihiyar kafar yaɗa labarai data rawaito wannan labari.
Haka zalika Alkalanci ta duba shafin ma’aikatar harkokin wajen Burkina Faso da na gwamnatin ƙasar amma babu makamancin wannan labari.
Sakamakon bincike:
Kasancewar wannan labari ne mai girma wanda kuma kasa ganin shi a sahihan kafafen jaridu na nuna cewa labarai. Yana da alamar tambaya. Bisa kasa samun inda wannan labarin ya fito yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa haɗa shi akai.