Hukunci: Gaskiya ne
Bisa kalaman Binta Farouk Jalingo na cewa ta bar Musulunci ta koma Kirista tun shekarar 1999 yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin barin Musuluncin Binta Farouk gaskiya ne amma ba a shekarar 2025 ta bar Musulunci ba.
Wasu shafukan sada zumunta sun yaɗa labarin cewa wata mai suna Binta Farouk ta bar Musulunci ta koma Kirista, labarin ya ƙara da cewa ma’aikaciyar gidan talabijin na NTA ce a Abuja.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna Arewa media ya wallafa cewa; “YANZU-YANZU: Fitacciyar Ma’aikaciyar Gidaɲ Talabijin A Tarayyar Najeriya Abuja, Hajiya. Binta, Ta Fìtà Daģa Addînîn Mùsùlùncì Zuwa Addînîn Ķìrìstà.
Wannan wallafa ta sami tofa albarkacin baki wato comments sama da dubu ɗaya cikin ƙasa da awa ɗaya da wallafawa.”

Haka zalika wannan shafin na Facebook mai suna Katsina online shima ya wallafa wannan labari duk da cewa a cikin hoton da aka wallafa tare da rubutun ya ce a NTA Yola ne.
Wani shafin daban mai suna Alfijir shima ya wallafa wannan labarin inda cikin awanni biyu mutane sama da dubu biyu suka tofa albarkacin baki wato comments.
Bincike:
Alkalanci ta fara da bincike ko akwai wata mai suna Binta Farouk kuma shin ita ce a hoton da ake yaɗawa? Alkalanci ta gano cewa hoton wacce ake yaɗawa tabbas sunan ta Binta Farouk, kuma tayi digiri a aikin jarida.
Sannan binciken Alkalanci ya kasa tabbatar da cewa tana aiki a NTA Abuja a yanzu haka, domin Alkalanci ta tuntuɓi ma’aikatan NTA sama da goma a Abuja amma babu wanda ya santa ko kuma ya san sunanta a Abuja.
Sai dai binciken Alkalanci ya tabbatar da cewa ta taba aiki da NTA Yola shekaru sama da ashirin baya.
To amma binciken Alkalanci ta bakin ita kanta Binta Farouk Jalingo ya tabbatar da cewa ta bar Musulunci tun shekarar 1999, shakara ɗaya bayan bayan ta haifi tagwaye wanda mijinta ya kwace su.
Wacece Binta Farouk Jalingo?
Sunan babban Binta Farouk Jalingo shine Major Usman Farouk Jalingo, an haife ta a barikin soji na Ikeja dake Lagos a watan Afrilun shekarar 1959.
Tayi karatun digiri a aikin jarida a jami’ar Najeriya dake Nnsukka jihar Enugu.
Ta auri Umar Farouk El-Kanami a shekarar 1997.
Ta haifi tagwaye a shekarar 1998, sai kuma ta bar Musulunci a shekarar 1999.
Sakamakon bincike:
Bisa kalaman Binta Farouk Jalingo na cewa ta bar Musulunci ta koma Kirista tun shekarar 1999 yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin barin Musuluncin Binta Farouk gaskiya ne amma ba a shekarar 2025 ta bar Musulunci ba.
