Hukunci: Ƙarya ne
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gano cewa wani shafin Tiktok mai suna Epic Motors Moves ne ya fara wallafa bidiyon makabartar motoci kirar Mercedes Benz, kuma ya bayyana cewa a kasar China gurin yake. Wannan yasa ikirarin cewa motocin na gidan marigayi Mai Deribe ne a Maiduguri karya ne.
Ikirari:
Akwai wani shafin Tiktok mai suna @abbasecmaina wanda ya wallafa wani bidiyo da aka ga tsoffin motoci kuma ya rubuta ikirarin cewa tsoffin motocin a gidan Marigayi Mai Deribe dake Maiduguri ne.
Wani shafin Facebook mai suna Muhammad T. Shehu ya wallafa wannan bidiyo. Sama da mutane dubu casa’in ne suka kalli bidiyon.((https://www.facebook.com/share/v/15SoVM3kDd/?mibextid=wwXIfr))
Shima wani shafin na Facebook mai suna Haruna Isa Darazo shima ya wallafa wannan bidiyo da ikirarin cewa motocin a gidan Mai Daribe ne.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba bidiyo a shafin samo asalin hotuna da bidiyo da kuma inda ya fito, inda ta gano cewa wani shafin Tiktok da ke wallafa motoci musamman kirar Mercedes Benz mai suna @EpicMotorMoves ya wallafa wannan bidiyo. Shafin dai ya bayyana inda motocin suke a matsayin makabartar mota kirar Mercedes Benz.
Mutane sama da miliyan biyu ne suka kalli bidiyon a shafin.
Bayan tambaya a shafin wanda aikin sa dama sanya motoci iri-iri kan a ina wadannan motoci suke sai shafin ya bada amsar cewa a kasar China ne.
Shafin ya kara wallafa bidiyo da ke nuna cikin wadannan motoci.
A iya bincike babu inda Alkalanci ya samo bidiyon da ya tabbatar da cewa wannan bidiyo ya fito ne daga Maiduguri, domin kuwa shafin Epic Motors Moves shine ya fara wallafa wannan bidiyo wanda wasu shafuka suka dauka tare da kara wallafa shi.
Sakamakon bincike:
Bisa samun asalin inda aka fara wallafa bidiyon, shafi ne da suka shahara wajen wallafa bidiyo da hotunan da suka danganci mota kirar Mercedes Benz da sauran su, shafin ya kuma wallafa bidiyon motoci a salo da dama harda cikin motocin wanda aka ga hannun bature yana budewa, da kuma rashin samun sahihin labarin da ke nuna cewa daga Maiduguri bidiyon ya fito. Wannan ya sa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin cewa bidiyon motocin na marigayi Mai Daribe a Maiduguri karya ne.
