Hukunci: Ƙarya ne
Kasancewar tun shekarar 2016 wato sama da shekaru biyar kafin zaman Ibrahim Traore shugaban ƙasa, mata masu ciki, haihuwa da yara ƴan ƙasa da shekaru biyar na samun kulawar lafiya kyauta a ƙasar Burkina Faso, wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ƙokarin yaudarar mutane ne.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna ATP Hausa ya wallafa cewa; shugaban kasar Burkina Faso ya ayyana haihuwa kyauta a asibitocin kasar.
Wannan wallafa ta sami shares sama da dari hudu Sai kuma comments sama da dari biyar.
Wani shafin ma mai suna Hausa News reporters ya wallafa irin wannan labarin.
Shima shafin Facebook mai suna Jakada Radio Television JRTV ya wallafa wannan labari.
Haka zalika shafin Instagram mai suna Hausa Room shima ya wallafa irin wannan labari. Labarin ya sami likes sama da dubu uku.
Bincike:
Kafar tantance labarai, bin diddigi da bincike ta Alkalanci ta bincika tare da samo bayanin cewa, a shekarar 2016 kasar Burkina Faso ta ayyana shirin bada kulawar lafiya kyauta, ga yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar da kuma mata masu juna biyu mai suna gratuite.
Rahoton ya nuna ƙasar ta Burkina Faso na bada kulawar lafiya kyauta ga mata sama da shekaru ashirin da suka gaba.
Wannan shirin da aka ƙaddamar a shekarar 2016 ya baiwa mata masu juna biyu, masu shayarwa da kuma yara ƴan ƙasa da shekaru biyar damar samun kulawar lafiya a ƙanana da manyan asibitocin ƙasar kyauta.
Alkalanci ta duba shafin hukumomin ƙasar ta Burkina Faso da sahihan gidajen jaridun ƙasar dama na waje amma ba’a sami inda aka rawaito cewa shugaba Ibrahim Traore ne ya ayyana wannan shiri ba.
Sakamakon bincike:
Bisa samun sahihan rahotanni da rubuce-rubucen cibiyoyin lafiya da ya bayyana cewa baiwa mata da ƙanana yara kulawar lafiya kyauta a ƙasar Burkina Faso ya daɗe da aka ayyana shi shekaru kafin Ibrahim Traore yayi juyin mulki. Sannan babu wata sahihiyar kafar jarida a Burkina Faso data rawaito cewa shugaba Ibrahim Traore yayi jawabin da ake iƙirari. Kafar Alkalanci ta yanke hukuncin cewa iƙirarin cewa Traore ya ayyana haihuwa kyauta a ƙasar ƙoƙari ne na yaudarar mutane ne.
