BindiddigiShin Shugaban ƙasa zai iya dakatar da gwamna?

Shin Shugaban ƙasa zai iya dakatar da gwamna?

-

Hukunci: Ƙarya ne
Kasancewar kundin tsarin mulki bai baiwa shugaban kasa da ma ba wajen dakatar da zababben gwamna. Yasa Alkalanci cewa shugaban kasa bai da hurumi.

A ranar 18 ga watan Maris na 2025 shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar Ribas tare da dakatar da gwamna da mataimakiyar sa da ƴan majalisar dokokin jihar.

Tuni dai Tinubu ya naɗa tsohon hafsan sojin ruwa Ibok-Ete Ibas a matsayin shugaban a jihar.

Yayin jawabi ga ƴan Najeriya kan wannan mataki Tinubu yace yayi hakan ne bisa ƙarfin da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya bashi.

Akwai dai rabuwar kai tsakanin ƴan Najeriya kan wannan dakatarwa da kuma ayyana dokar ta ɓacin.
Wasu ƴan ƙasar na ganin ya sabawa doka wasu kuma na ganin shugaba Tinubu na kan dai-dai.
A shekarar 2004 shugaba Olusegun Obasanjo ya taɓa dakatar da gwamnan jihar Filato Joshua Dariye.
Sai kuma a shekarar 2006 nan ma ya dakatar da gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose

Me kundin tsarin mulkin yace?

Sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa shugaban ƙasa damar sanya dokar ta ɓaci idan akwai babban rikici a jiha. To sai dai wannan sashe bai baiwa shugaban ƙasa damar ko ƙarfin iya dakatar ko cire gwamna ba.
Hasali ma sashen kundin tsarin mulki na 188 da na 189 dakatar da gwamna ko cire shi aiki ne na majalisar dokokin jihar.
Haka zalika sashen na 11 (4) na kundin tsarin mulkin ya baiwa majalisar dokokin ta ƙasa da ta ɗauki ayyukan majalisar dokokin jihar idan har majalisar dokokin sun kasa ko ba zasu iya gudanar da ayyukan su ba.
Kuma tsarin mulkin Najeriya bai baiwa shugaban ƙasa damar dakatar da ayyukan majalisar dokokin jihar ba, domin kuwa yin hakan aiki ne na bangaren Shari’a da kuma majalisa ba harkar sashen zartaswa na ƙasa bane.
Kungiyar lauyoyi ta Najeriya NBA tayi Allah wadai da dakatar da zababben gwamna, mataimakiyar sa da kuma yan majalisar dokoki inda kungiyar ta bayyana hakan a matsayin haramtaccen mataki, wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Shugaban kungiyar ta kasa Afam Osigwe SAN yace shugaban kasa bashi da hurumin dakatar da zababben gwamna, mataimakiyar gwamna da kuma zababbun ‘yan majalisar dokikin jiha.

Me doka tace kan sanya dokar ta ɓaci?

Duk da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya baiwa shugaban ƙasa damar ayyana dokar ta ɓaci.
To amma dole sai ya miƙa wannan buƙata ga shugaban majalisar dattawa da na  wakilai idan ana so ta zama halattacciyar doka.
Sashe na 305 (3) wanda ya haɗa daga (a zuwa g)  ya bayyana rikicin da ka iya sanyawa a ayyana dokar ta ɓaci.
  1.  Idan ƙasa tana cikin yanayin yaƙi.
  2.  Idan ƙasa na cikin barazanar mamaya ko fadawa cikin yaƙi.
  3. Idan taɓarɓarwar doka da oda, rashin tabbas na tsaron lafiyar mutane a ƙasa ko wani sashe na ƙasa wanda dole a ɗauka mataki mai tsauri domin dawo da zaman lafiya.
  4. Idan akwai tabbacin wani haɗari na rashin bin doka da oda, wanda akwai buƙatar daƙile yiwuwar hakan.
  5. Idan haɗari, ko wani babban ibtila’i da ya sami wani yanki na ƙasa.
  6.  Idan akwai kowanne irin matsala da ka iya yin barazana ga kasancewa Najeriya dunkulalliyar ƙasa.
  7.  Idan shugaban ƙasa ya sami rokon buƙatar hakan, wanda yayi dai-dai da ƙaramin sashe na 4 cikin baka.

Sakamakon bincike:

Kasancewar duk da kundin tsarin mulki ya baiwa shugaban ƙasa damar sanya dokar ta ɓaci a jiha amma bai bashi damar dakatar da zaɓaɓɓen gwamna da majalisar dokokin jihar ba, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa a doka shugaban ƙasa bashi da damar dakatar da zaɓaɓɓen gwamna ko majalisar dokokin jiha.
Labarai masu alaka: 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa wani labari tare da hotuna wanda ya yadu matuka da...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da suka bayyana cewa ‘yan Najeriya sunyi asarar makudan kudade yayin...

Cirani: Shin Tarayyar Turai ta amince ‘yan Afrika su tsallaka ta Libya ba tare da Biza ba?

Duk da cewa kasashen turai na nuna damuwa tare da daukar matakan rage shigar bakin haure, ‘yan cirani dake...

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

  Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da...

Karanta wannan

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar