Hukunci: Ƙarya ne
Binciken Alkalanci ya ga no cewa babu wani sahihin bincike da ya nuna cewa ruwan AC na da tsaftar amfani a cikin batiri balle sha. Domin kuwa yana dauke da kwayoyin cuta, karfe da sauransu wadanda ke da illa. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin karya ne.
Akwai dai wasu ikirarai dake yawo a kafafen sada zumunta da dama dake nuna cewa ruwan dake fitowa daga na’urar sanyaya guri wato AC nada tsafta kuma za’a iya amfani dashi a batirin mota wasu ma sunce yana da amfani Idan aka sha shi.
Wani shafi Facebook mai suna Deejarh Berver ya wallafa bidiyo dauke da ikirari da dama kan muhimmancin ruwan AC.

A bidiyon wanda ya sami share sama da dari uku likes sama da dubu hudu da kuma wadanda suka kalla sama da dubu dari da casa’in. Ya ce suna siyen lita ashirin da biyar a kudi naira dubu dari da tamanin da biyar (N185,000)
Shima wani shafin daban ya tu ikirarin cewa; yana da tsafta da kuma amfani.

Wannan ikirari dai ya wuce Facebook domin yana yaduwa matuka da WhatsApp, Tiktok da sauran shafuka.
Bincike:
Kafar tantance labarai dai ta gano cewa duk da cewa ruwan dake fitowa daga AC yana fitowa ta hanyar zafi ne wanda ake cewa na tsaftace ruwa to amma ba daidai take da yadda ake tsaftace ruwa din ba.
Ba kamar yadda ake dafa ruwa domin tsaftace shi ba, shi ruwan AC na bin hanyoyin da ke haduwa da wasu kwayoyin cututtuka, kura, robobi, baraguzan tsatsar karfe da sauran kananan halittu.
Binciken masana ya nuna cewa ruwan AC na dauke da wasu kwayoyin halitta masu hatsari ga batari dama lafiyar mutane misali; Legionella, Mycobacterium wanda ke da hatsari wajen amfani a batir da duk wani amfani da ake cewa za’ayi dashi.
A watan Mayun 2025 gidan jaridar Indian Times tayi bincike inda ta rawaito hatsarin dake tattare da amfani da ruwan AC a batir. ((https://timesofindia.indiatimes.com/technology/appliances/is-it-safe-to-use-ac-discharge-condensed-water-for-inverter-batteries/articleshow/121511004.cms))
Dr. Hajar Mamman Nassir kwararriyar likita ce a Abuja tace shan ruwan AC na da illa ga lafiyar mutum matuka. Ta ce inda kawai za’a iya amfani da ruwa AC sune;
Wanke mota, wanke simintin gida, ban ruwan fulawowin da basa fitar da abinda za’a sha ko ci, sai kuma amfani wajen kora kashi a ban daki.
Sakamakon bincike:
Babu dai wani bincike da ya nuna cewa ruwan AC na da tsaftar amfani a cikin batiri balle sha. Domin kuwa yana dauke da kwayoyin cuta, karfe da sauransu wadanda ke da illa.
Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin tsaftar ruwan AC domin sha da sanyawa a batiri karya ne.
