BindiddigiShin Ribadu Ya Ce Tinubu Na Cikin Jerin Masu...

Shin Ribadu Ya Ce Tinubu Na Cikin Jerin Masu Rashawa?

-

Nuhu Ribadu ya kasance tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC. wanda yanzu shine mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Ikirari:

Akwai wani bidiyo dake yaduwa a kafar sada zumunta da dama inda Naja’atu Mohammed ke cewa mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro NSA Nuhu Ribadu lokacin yana shugaban EFCC ya taba ayyana shugaba Bola Tinubu a matsayin daya daga cikin wadanda ake zargi da rashawa da almundahana lokacin Tinubu na Gwamnan jihar Legas.
A bidiyon dai an ji Naja’atu na zargin cewa, Ribadu ya bayyana Tinubu a matsayin Gwamnan da ke kan gaba wajen cin hanci a lokacin da ya ke gwamnan Legas shi kuma Ribadu ke rike da shugabancin EFCC.

Jaridu da dama sun buga wannan labari harda jaridar Daily Trust, cikin bidiyon TikTok ɗin, Naja’atu ta zargi Ribadu da yin aiki a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, bayan ya soke shi sau da dama a lokacin da ya ke Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) a shekarun baya.

To sai dai shi kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya musanta hakan, a cikin wata wasiƙa ta hannun lauyansa, Ahmed Raji, Ribadu ya bayyana cewa, a fili ko a sirrance, bai taɓa sukar Tinubu ba a lokacin da ya ke shugabantar EFCC.
Ribaɗu ya ce bai taɓa ko da sau ɗaya ba suka, tsakala ko tona wani zargin kan almundaha a lokacin Tinubu na gwamnan Legas.

Bincike:

Kafar tantance labari, bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta fara da binciken ko Nuhu Ribadu ya taba yin magana kan zargin rashawa ko almundahana da ake zargin Tinubu lokacin yana shugaban EFCC.

A binciken Alkalanci ta sami labarin da gidan jarida na Vanguard ya wallafa a ranar 19 ga watan Fabrairun shekarar 2007 inda yace gwamnonin jihohi a Najeriya a wancan lokaci irin su Bola Tinubu na jihar Legas, Orji Kalu na jihar Abia, Ibrahim Shekarau na jihar Kano, da sauran su za’a gurfanar dasu saboda ana zargin su da almundahana.

Hoton labarin jaridar Vanguard na shekarar 2007.
Hoton labarin jaridar Vanguard na shekarar 2007.
Haka zalika mun samo shafi a jaridar Daily Trust da aka buga a watan Fabrairun shekarar 2007. Inda a cikin labarin ya nuna yadda Nuhu Ribadu lokacin yana shugaban EFCC yace hukumar ta EFCC zata cigaba da bibiyar gwamnoni sau da kafa domin ganin an gurfanar dasu a gaban koto saboda zargin rashawa da almundahana.
Cikin wadanda aka wallafa cewa Nuhu Ribadu ya fada a matsayin wadanda ake zargin almundahana da rashawa a labarin sun hada da Bola Tinubu na Legas, Orji Kalu na Abia, Ibrahim Shekarau na jihar Kano.
Cikin labarin yace “Tinubu da sauran gwamnoni sunyi sa’a sosai domin da tuni sun shiga sahun tsigaggun gwamnonin jihar Filato Joshua Dariye, Ayodele Fayose na Ekiti da DSP Alamaisiegha na jihar Bayelsa. Bazasu gujewa hukuma ba.”
Hoton labarin jaridar Daily Trust na shekarar 2007.
Hoton labarin jaridar Daily Trust na shekarar 2007.
Wadannan bayanai na Ribadu da jaridun biyu suka buga ya yisu ne a filin sauka da tashin jaragen sama na Murtala Mohammed dake Legas.
Gidan jarida na VOA shi ma ya wallafa labarin yadda Nuhu Ribadu ya zargi gwamnoni da almundahana yayin zaman kwamitin majalisar dattawa a shekarar 2009.
Sannan kafar tantance labarai ta Alkalanci ta samo wani labari da jaridar Vanguard ta wallafa a shekarar 2009 inda anan ma an wallafa yadda Ribadu ya zargi wasu gwamnoni da almundahana lokacin yana shugaban EFCC.

Sakamakon bincike:

Bisa samun labarai daga manyan jaridu na inda Nuhu Ribadu ya bayyana Bola Tinubu da wasu gwamnoni a matsayin wadanda ake zargin almundahana da rashawa. Yasa kafar tantance labarai bindiddigi da bincike ta Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin da Naja’atu Mohammed tayi na cewa Nuhu Ribadu ya taba ayyana Tinubu da wasu gwamnoni a matsayin wadanda ake zargi da rashawa da almundahana gaskiya ne.
Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa wani labari tare da hotuna wanda ya yadu matuka da...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da suka bayyana cewa ‘yan Najeriya sunyi asarar makudan kudade yayin...

Cirani: Shin Tarayyar Turai ta amince ‘yan Afrika su tsallaka ta Libya ba tare da Biza ba?

Duk da cewa kasashen turai na nuna damuwa tare da daukar matakan rage shigar bakin haure, ‘yan cirani dake...

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

  Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da...

Karanta wannan

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar