Akwai dai zarge-zarge tsakanin gwamnatin Najeriya da Nijar tun bayan juyin mulki da sojoji sukayi a kasar, wanda ke rura wutar labaran karya dangane da kasashen biyu.
Batu:
Akwai wani shafin Facebook mai suna Damagaram Post ya wallafa wani ikirari (archived here) a ranar lahadi 22/12/2024 inda ya rubuta cewa “ 🛑Nijar zata gina katanga mai tsawon Km 1497 a iyaka tsakaninta da Nigeria domin karfafa tsaro a kasar.”
W annan wallafa dai ta sami tofa albarkacin baki sama da dari uku kasa da mintuna talatin da wallafawa.
Bincike:
Kafar bindiddigi ta Alkalanci ta tuntubi mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Nijar Amadou Ango Souley ((Responsable de la communication du Ministère des Affaires Étrangères auprès du Ministre)) data tambayeshi cewa baya ga zarge-zargen da sukewa gwamnatin Najeriya akwai shirin gina katanga tsakanin Nijar da Najeriya? Sai yayi dariya yace “wannan magana ce kawai babu wani shiri irin wannan, shirmen ‘yan kafafen sada zumunta ne kawai.”
Sakamakon Bincike:
Bisa bayanan mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta Nijar din na cewa babu wani shiri makamancin haka yasa kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne.