Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar ta bar harshen Faransanci.
To sai dai ba kamar yadda wasu suka fahimci labarin ba ga yadda abin yake.
A yanzu dai kasar ta Nijar ta tabbatar da cewa Hausa ta zama harshen ƙasa wato langue nationale a Faransanci.
Wannan na nufin cewa harshen Hausa an amince shi a matsayin harshen da ke da muhimmanci wajen adana al’adu, sadarwa a tsakanin jama’a, da koyar da ilimi a matakin farko wato firamare amma hakan ba yana nufin baza’a koyar da yaren Faransanci ba. Haka zalika kasar ta bayyana wasu yaruka a kasar a matsayin masu muhimmanci.
Amfani da Hausa a matsayin harshen ƙasa yana nufin za a iya amfani da shi a:
Makarantun firamare.
Za’a dinga sadarwa da shirye-shirye a rediyo da Talabijin.
Tattaunawa tsakanin al’umma da hukumomi a matakin ƙasa.
Wayar da kan mutane kan wasu al’amuran da suka shafe su ko suka shafi kasa.
To amma inda gizo ke sakar shine harshen Faransanci har yanzu shine harshen aiki wato langues de travail a Faransanci.
Faransanci shine harshen da gwamnati za ta cigaba da amfani da shi wajen:
To amma fa baya ga Faransanci kasar ta kara da Turancin Ingilishi a matsayin harshen gwamnati.
sune dai za’a dinga;
Rubuce-rubuce a hukumance.
Takardun gwamnati da dokoki.
Tattaunawa da kasashen waje.
Zaman kotu da yanke hukunci a kotu.
Rubutu da karatu a jami’o’i da sauran manyan makarantu.
Kasar ta Nijar dai ba ta cire Faransanci a matsayin yaren gwamnati ba sai dai kara harshen turancin Ingilishi kamar yadda kasar Algeria tayi inda ake koyar da yara yarukan biyu a makarantu.