Hukunci: Ƙarya ne
Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirari cewa Najeriya ce ta uku cikin ƙasashen da aka fi kai hare-haren ta'addanaci a duniya ƙarya ne.
Najeriya dai na cikin ƙasashen duniya dake fama da matsalar tsaro da hare-haren ta’addanci wanda wasu lokuta kan haddasa labaran ƙarya kan matsalar musamman abinda ya shafi alƙaluma.
Iƙirari:
Akwai dai wani rahoto da gidan jarida na BBC Hausa ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar 7/03/2025 inda cikin rahoton yace Najeriya ce ta uku cikin ƙasashen da aka fi kai hare-haren ta’addanaci a duniya sai kuma ƙasar Nijar ta biyar.
Wallafar dai ta sami tofa albarkacin baki wato comment dubu daya da dari biyar da kuma shares sama da dari da casa’in.

Bincike:
Kafar tantance labarai, bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta duba rahoton ayyukan ta’addanci na duniya wato Global Terrorism index wanda aka wallafa a ranar 5/03/2025.
A cikin rahoton dai Alkalanci ta gano cewa Najeriya ce ƙasa ta biyar cikin ƙasashen da aka fi kai hare-haren ta’addanaci a duniya maimakon ta uku da BBC tayi ikirari wacce take biwa ƙasar Nijar wacce take a matsayi na biyar.

Rahoton dai ya ce an sami raguwar hare-haren ta’addanci da kashi 37 to amma kashe-kashe ya karu da kashi 6 wanda rahoton yace mutanen da suka mutu sanadiyyar ta’addanci sun kai 565 a shekarar 2024. Wanda shine mafi yawa tun shekarar 2020.
Rahoton ya alakanta hakan da rikici tsakanin mayakan Boko Haram da ISWA, domin kuwa kashe-kashe dake da alaka da kungiyoyin biyu shine kaso mafi girma wato kashi 60.

Yaushe aka wallafa rahoton?
Sannan a rahoton na BBC sun bayyana cewa an wallafa rahoton a 5 ga watan Mayu duk da cewa ba’a rubuta watan Mayun wacce shekara ba. To sai dai Alkalanci ta gano cewa rahoton dai an wallafa shi ne a 5 ga watan Maris din shekarar 2025.
Sakamakon bincike:
Bisa alkaluman da rahoton na GTI ya fitar, a gaba daya cikin rahoton babu inda aka bayyana Najeriya a matsayi kasa ta uku cikin jerin ƙasashen da aka fi kai hare-haren ta’addanaci a duniya. Rahoton ya sanya ta a matsayi na shida wato tana biwa Nijar dake matsayi na biyar.
Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirari cewa Najeriya ce ta uku cikin ƙasashen da aka fi kai hare-haren ta’addanaci a duniya ƙarya ne.