BindiddigiShin Najeriya ce ta uku cikin ƙasashen da aka...

Shin Najeriya ce ta uku cikin ƙasashen da aka fi kai hare-haren ta’addanaci a duniya?

-

Hukunci: Ƙarya ne
Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirari cewa Najeriya ce ta uku cikin ƙasashen da aka fi kai hare-haren ta'addanaci a duniya ƙarya ne.
Najeriya dai na cikin ƙasashen duniya dake fama da matsalar tsaro da hare-haren ta’addanci wanda wasu lokuta kan haddasa labaran ƙarya kan matsalar musamman abinda ya shafi alƙaluma.

Iƙirari:

Akwai dai wani rahoto da gidan jarida na BBC Hausa ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar 7/03/2025 inda cikin rahoton yace Najeriya ce ta uku cikin ƙasashen da aka fi kai hare-haren ta’addanaci a duniya sai kuma ƙasar Nijar ta biyar.
Wallafar dai ta sami tofa albarkacin baki wato comment dubu daya da dari biyar da kuma shares sama da dari da casa’in.
Labarin dake yaduwa.
Labarin dake yaduwa.
Bincike:
Kafar tantance labarai, bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta duba rahoton ayyukan ta’addanci na duniya wato Global Terrorism index wanda aka wallafa a ranar 5/03/2025.
A cikin rahoton dai Alkalanci ta gano cewa Najeriya ce ƙasa ta biyar cikin ƙasashen da aka fi kai hare-haren ta’addanaci a duniya maimakon ta uku da BBC tayi ikirari  wacce take biwa ƙasar Nijar wacce take a matsayi na biyar.
Rahoton GTI dake nuna Najeriya ce ta shida,
Rahoton GTI dake nuna Najeriya ce ta shida,
Rahoton dai ya ce an sami raguwar hare-haren ta’addanci da kashi 37 to amma kashe-kashe ya karu da kashi 6 wanda rahoton yace mutanen da suka mutu sanadiyyar ta’addanci sun kai 565 a shekarar 2024. Wanda shine mafi yawa tun shekarar 2020.
Rahoton ya alakanta hakan da rikici tsakanin mayakan Boko Haram da ISWA, domin kuwa kashe-kashe dake da alaka da kungiyoyin biyu shine kaso mafi girma wato kashi 60.
Rahoton GTI kan ta’addanci a Najeriya.
Rahoton GTI kan ta’addanci a Najeriya.

Yaushe aka wallafa rahoton? 

Sannan a rahoton na BBC sun bayyana cewa an wallafa rahoton a 5 ga watan Mayu duk da cewa ba’a rubuta watan Mayun wacce shekara ba. To sai dai Alkalanci ta gano cewa rahoton dai an wallafa shi ne a 5 ga watan Maris din shekarar 2025.

Sakamakon bincike:

Bisa alkaluman da rahoton na GTI ya fitar, a gaba daya cikin rahoton babu inda aka bayyana Najeriya a matsayi kasa ta uku cikin jerin ƙasashen da aka fi kai hare-haren ta’addanaci a duniya. Rahoton ya sanya ta a matsayi na shida wato tana biwa Nijar dake matsayi na biyar.
Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirari cewa Najeriya ce ta uku cikin ƙasashen da aka fi kai hare-haren ta’addanaci a duniya ƙarya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar