Akwai dai tataburza a wasu jihohin Najeriya inda wasu ke ganin cewa jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa wato road safety ba zasu iya aiki a kan hanyoyi mallakar jiha ba, duk da cewa ana ganin su a cikin gari suna tsare masu abun hawa tare da cin tararsu.
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba wannan lamari inda ta fara da samun sakamakon wata shari’a da kotun daukaka kara dake Asaba jihar Delta tayi a shekarar 2023 wanda tace jami’an na road safety basu da hurumin yin aiki ko kama musu abun hawa a hanyoyi dake mallakar jihohi.
Kotun tayi watsi da daukaka karar hukumar ta FRSC kan shari’a tsakanin hukumar ta FRSC da wani mai suna Darlington Ehikim, shari’a mai lamba CA/AS/276/2019 wacce a baya kotun tarayya dake Owerri ta ce hukumar bata da hurumin aiki a hanyoyin jihohi.
Kotun ta ce jami’an na iya aiki ne kawai a hanyoyi mallakar gwamnatin tarayya.
Hukuncin kotun ya nuna cewa duk jami’an road safety da sukai aiki a hanyoyi mallakar jiha haramtaccen aiki ne kawai sukeyi.
Kotun daukaka kara a Abuja
To amma a wata shari’a da kotun daukaka kara dake Abuja tayi a shekarar 2024 tace jami’an hukumar na FRSC na iya aiki a dukkan hanyoyin Abuja Kasancewar hanyoyin Abuja suma mallakar gwamnatin tarayya ne.
Kotun tarayya a Bauchi
Kotun tarayya a Bauchi
Haka zalika a wannan shekarar ta 2025 wata kotun tarayya dake Bauchi ta fitar da wata shari’a dake cewa jami’an FRSC na iya aiki a kowacce irin hanya ta tarayya ko ta jiha amma kotun ta ce a jihar Bauchi.
Wacce ta jagoranci shari’ar mai shari’a Aisha Ibrahim tace masu kara Dr. Ibrahim Danjuma da wani basu bayar da cikakken shaidar cewa hanyar da suke korafin ta gwamnatin jiha ce.
Masana Doka
Masana Doka
Lauyoyi a Najeriya dai sun sha jadda cewa jami’an FRSC basu da hurumin aikin a hanyoyi mallakar jihohi wanda suka alakanta rashin sanin ilimin doka da kuma ‘yanci ke sa har jami’an na FRSac ke aiki ba tare da wani turjiya ba.
Yanzu haka ma dai wani lauya a jihar Kano mai suna Abba Hikima ya kai karar hukumar ta FRSC kan aiki a hanyoyi mallakar jiha.
Jami’an FRSC
To sai dai jami’an na FRSC na ganin killace su yin aiki a hanyoyin gwamnatin tarayya bazai haifar da da mai ido ba domin Idan anyi hatsari a hanyoyin jihohi suna kai mutane asibiti.
