A yayin da ake shirin zaben shugaban kasa a kasar Ghana ana cigaba da samun karuwar yaduwar ikirari da labarun karya domin bata wani dan takara Ko jamiyya ko kuma kambama jamiyya ko dan takara.
Batu:
Akwai wani ikirari dake yaduwa a kasar Ghana musamman a yankunan Hausawan kasar inda ake zargin jagora a jamiyyar NPP dake kula da yankunan Zango wanda mafi akasarin su musulmai da Hausawa ne Aziz Futa da cewa: “Duk Limami ko Sarkin Zango da bai zabi dan takarar shugaban kasa na jamiyyar NPP Dakta Bawumia ba wuta zai shiga.”
Wannan ikirari dai an sanyashi a matsayin hoto tare da sanya tambarin gidan talabijin na Ghana “GHONETV”.
Bincike:
Da farko dai kafar bindiddigi ta Alkalanci mun tuntuni dan jarida a kasar Ghana Idris Abdallah inda ya tuntubi gidan Talabijin na Ghana TV. Gidan Talabijin din dai sun karyata tare da bayyana cewa wannan ikirari da hoto da aka sanya sunansu ba daga gare su bane.
Haka zalika sun kara da cewa tuni sun gayyaci Aziz Futa wanda ya nesanta kansa da wadancan bayanai.
“Ni ba malami bane balle na bada wannan fatawa, ni kuma ba Allah bane- balle nasan wadanda zasu shiga wuta Ko Aljannah, ban taba wannan magana ba Sam-Sam, an shafa min ne. Maganar dana fadi shine in yau chief imam ya zama flag bearer na NPP mun sami yan Zango musulman da zasu ce ba musulmin kirki bane, yana bautar turu, bai sallah bai kaza just because ya zama NPP wanga magana na fada kuma nayi repeating.”
Sakamakon Bincike:
Kafar bindiddigi ta Alkalanci bayan bincike inda aka kasa samo faifan sauti inda ya fadi wadancan kalamai, kuma gidan Talabijin na Ghana suka karyata cewa ba daga gurinsu bane haka sannan shi kansa Aziz Futa ya fadi kalaman daya fada, ta yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne wato Aziz Futa baiyi wadancan kalamai shiga wuta ba.