BindiddigiShin dagaske ne hada tumatir, coffee da lemun tsami...

Shin dagaske ne hada tumatir, coffee da lemun tsami na sa fatar mutum tayi laushi?

-

Hukunci: Ƙarya ne
Akwai dai bayanai  da dama na kula da lafiya dake yaduwa a kafafen sada zumunta wanda kuma basu da gurin zama a ilimin kimiyya wato dai na karya.

Akwai dai bayanai  da dama na kula da lafiya dake yaduwa a kafafen sada zumunta wanda kuma basu da gurin zama a ilimin kimiyya wato dai na karya.

ikirari:

Akwai dai wani bidiyo dake yaduwa a kafar sada zumunta ta TikTok inda wani shafi mai suna @drmaijalalaini  Ya wallafa. A cikin bidiyon dai anji yadda ake nuna cewa idan aka hada tumatir da coffee da kuma lemon tsami da suga da zuma yana magance bushewar fata tare da sa ta tayi laushi kamar ta jariri.
“ina wadanda ke fama da bushewar jiki, bushewar kafa to hanya mai sauki ne a nemo tumatur rabi a matse ruwansa, sai a kawo naskef cokali a zuba sai a kawo lemon tsami rabi a matsa, sannan a kawo suga karamin cokali a zuba, sai a zuba zuma karamin cokali, sai a juya shi, a juya sosai sai a rika shafawa a wurin. Bayan minti sha biyar a wanke.”

Bincike:

Kafar tantance labarai bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta gano cewa akwai irin wadannan bidiyo DIY do it yourself a turance  ma’ana dai yi da kanka maimakon zuwa wajen kwararre.
Akan haka ne muka tuntubi Zainab Bashir Ya’u kwararriyar likitar fatar mutum domin yin binciken sahihancin wancan bidiyon kuma ta bayyana mana cewa amfani da tumatir da coffee domin gyara busashshiyar fata bashi da wani tushe a ilimin kimiyya, domin kuwa akwai sinadaran da ke cikin tumatir da zasu iya lalata fata baki daya saboda karfin su.
Ta kara da cewa wannan DIY wato yi da kanka dinnan basu dace da ko wanne yanayin fata ba saboda haka gara mutum yaje yaga kwararre.

Sakamakon bincike:

Bisa kasa samun wani rahoto ki bincike na kimiyya da ya tabbatar da gaskiyar wancan ikirari da kuma bayanin Dr Zainab Ya’u wanda tace maimakon gyara wancan hadin ka iya illata fata. Don haka kafar tantance labarai,  bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta yanke hukuncin cewa ikirarin amfani da timatir da coffee da lemon tsami don sanya laushin fata karya ne.
Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

  Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da...

Najeriya-Saudiyya sun karyata labarin cewa za’a hana ‘yan kasar bizar shiga Saudiyya

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta karyata ikirarin karya da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda ke cewa...

Ina gaskiyar cewa Amurka, Faransa ke neman haddasa faɗa tsakanin Sudan da Chadi?

  Duk lokacin da aka sami wata hatsaniya ko rikici tsakanin kasashe, wasu na amfani da wannan dama wajen yada...

Bidiyon ƴan sanda sunyi kame a Edo ƙarya ne, bidiyon ya faru a Ghana ne

  A yayin da ƴan Najeriya ke cigaba da Allah wadai da kisan wasu matafiya a jihar Edo, wasu na...

Karanta wannan

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar