BindiddigiShin Daga Tutar Rasha A Arewa Yasa Aka Saka...

Shin Daga Tutar Rasha A Arewa Yasa Aka Saka Hausa A Kudin BRICS?

-

Kungiyar kasa da kasa ta BRICS dai a jiya laraba ta fitar da samfurin kudin kungiyar da zasu fara amfani dashi a kasuwancin kasa da kasa maimakon Dalar Amurka.
A sabon samfurin kudin dai anga tutocin kasashe da sunayen kasashe wanda ya hada da Najeriya.

Batu:

Wani mai suna Ali Suwaga Hausa 3 a wani bidiyo daya fitar mai tsawon mintuna 3 da sakan 56 a shafin TikTok yayi ikirarin cewa daga tutar kasar Rasha da ‘yan arewa sukayi shine musabbabin sanya tutar Najeriya dama rubutun Hausa.
Mun tsakuro abinda ya fada; “Akayi watsi da turanci, akayi watsi da yarabanci, akayi watsi da Ibanci, Wallahi Allah ba komai ya janyo ba kunga wannan zanga-zangar da mukai mukace a daga tutar rasha Jana’s suka daga tutar Rasha na rantse da Allah shine takai ta kawo bayan kirkiro kudin da akayi akasa Hausa kuma akasa jumhoriyar tarayyar Najeriya kuma aka makala tutar Najeriya waye yayi tunanin cewa za’a maka tutar Najeriya? Kunga shuwagabbin Najeriya a gurin? To batasu ake ba…” 
Wannan bidiyo dai ya sami yadawa wato shares sama da dubu uku sannan wasu mutane sama da dubu daya suka tofa albarkacin bakin su.
Misali wani mai suna Kamal Ibrahim yace “ KO yanzU yakamata yan Nigeria mu fita mu nuna jindadinmu da faruwan wannan alkhairin asake daga tutar Russia.

Bincike:

Cikin binciken da Alkalanci yayi shine ya gano cewa Kungiyar ta BRICS ta kara wasu kasashe 13 ciki harda Najeriya a matsayin abokan hulda (Partners) ba mambobin din-din-din ba. Kasashen sune;  Algeria, Belarus, Bolivia, Cuba, Indonesia, Kazakhstan, Malaysia, Nigeria, Thailand, Turkey, Uganda, Uzbekistan, Vietnam.
A taron kungiyar ta BRICS na shekarar 2023 da akayi a kasar Afirka ta Kudu shugaba Bola Tinubu ya tura mataimkinsa a matsayin wanda ya wakilce shi wanda a wannan taro ne dai kungiyar ta bayyana cewa kasashe sama da 12 sun nuna ra’ayin shiga kungiyar.
Haka zalika ministan harkokin wajen Najeriya a wata hira da kafar jarida ta Bloomberg yace Najeriya na kawo karfin da zata iya shiga wannan kawance Ko ace kungiya.
Idan muka dawo batun rubutun jikin samfurin kudin Alkalanci ya gano cewa duk kasashen da aka rubuta sunayensu da daya daga cikin yaren kasar akayi bana turawan mulkin mallaka ba.
Misali kasar Afirka ta kudi wacce itama kasa ce da take amfani da Ingilishi a matsayin yare a gwamnatance amma bashi akayi amfani dashi ba anyi amfani da yaren kasar da akafi amfani dashi a harkokin yau da kullum a kasar.

Sakamakon Bincike:

Alkalanci dai ya gano cewa ikirarin cewa zanga-zanga tare da daga tutar Rasha ce tasa aka saka Najeriya da rubutun Hausa karya ne wato false.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar