BindiddigiShin Cristiano Ronaldo Yayi Umrah?

Shin Cristiano Ronaldo Yayi Umrah?

-

A yan kwanakin baya dai wani tsohon abokin wasan shahararren dan wasan kwallon kafar nan Cristiano Ronaldo yana nuna sha’awar musulunci inda wasu har suka dinga yada cewa ya musulunta.

Batu:

Akwai wani shafin Facebook mai suna Damagaram Post ya wallafa wani rubutu (archived here) daka ikirarin cewa “ Ronaldo ya gudanar da Umarar farko bayan ya musulumta“  baya ga wannan ikirari akwai wasu hotuna dake dauke da siffar Cristiano Ronaldo harma da wata mace tare dashi a gaban ka’abah sanya da ihrami wanda duk wanda zaiyi Haj ko Umrah sai ya sanya.

Bincike:

Kafar bindiddigi ta Alkalanci tayi amfani da manhajojin duba hotuna inda ta gano cewa hoton dai kirkirarren hoto ne da akai amfani da fasahar AI wajen hadawa wanda dakyar mutane zasu iya banbance na karya da gaskiya wato “deep fake” a turance.
Haka zalika da kafar Alkalanci tayi amfani da sashen binciken hotuna na google babu wata sahihiyar kafar yada labarai a kowanne yare data wallafa hoton ma balle labarin.

Sakamakon bincike:

Bisa gano cewa hoton hadadden hoto ne da akayi amfani da kirkirarriyar fasahar AI aka hada abinda ake kira “deep fake” yasa kafar Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan labari dama hoton karya ne.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa wani labari tare da hotuna wanda ya yadu matuka da...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da suka bayyana cewa ‘yan Najeriya sunyi asarar makudan kudade yayin...

Cirani: Shin Tarayyar Turai ta amince ‘yan Afrika su tsallaka ta Libya ba tare da Biza ba?

Duk da cewa kasashen turai na nuna damuwa tare da daukar matakan rage shigar bakin haure, ‘yan cirani dake...

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

  Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da...

Karanta wannan

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar