BindiddigiShin Ana Maida Agwaluma GMO Ta Amfani Da Allura?

Shin Ana Maida Agwaluma GMO Ta Amfani Da Allura?

-

Batun sabbin nau’ikan kayan marmari da dabbobi da aka sauyawa kwayar halitta da ake kira da GMO batune da ake ta magana tare da nuna shakku akai a ‘yan shekarun nan.

Batu:

Akwai wani bidiyo da yake yaduwa a kafar tura sakwanni na WhatsApp da a cikin bidiyon ake nuna agwaluma tare da ikirarin cewa an yiwa agwaluman allura wanda ya maida shi GMO.
Jiya muna dawowa gida yara suka ga agwaluma muka tsaya aka sai musu sai suka ce tana da dan ciwo a canza, bayan duk canzawar sai na karba sai nake ganin wannan abinda ake fada na GMO dukkan wannan ba ciwo bane, allure ce akewa fruits da kayan abinci domin ayi modifie din élément domin suyi saurin nuna ba tare da sun dau time da naturally suke ba...”

Bincike:

Kafar tantance labarai, bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta binciki yadda ake hada ko samun GMO inda hukumar kula da abinci ta Amurka ta bayyana yadda ake samar da kayan marmari abinci ko naman GMO.
Kwararru dai na cirar kwayar halitta domin sanya wannan kwayar halitta a cikin irin abinda ake son sauya kwayar halitta, wasu lokutan kuma ana iya cire wata kwayar halitta ne daga cikin wannan iri.
Ana dai daukar kwayar halitta ta hatsi, bishiya, kayan marmari harma dabbobin da ake bukata sai a sanya a wani daban domin samun sabon kala.
Yadda ake samar da GMO.
Yadda ake samar da GMO.
Haka zalika Alkalanci ta tuntubi shugaban hukumar bunkasa fasahar halittu Farfesa Abdullahi Mustapha inda ya bayyana cewa ba’a yiwa kowanne irin halitta na kayan marmari allura domin canza musu halitta don zama GMO su nuna da wuri.
Yadda ake samar da GMO daban domin batune na ammafani da kwarewa ta kimiyya da fasaha wajen sanya kwayar halitta a cikin irin da ake so a samar na GMO. Babu batun yiwa kayan marmari allura don zama GMO ko don yayi saurin nuna.”
Alkalanci ta samo labarin da hukumar kula da abinci da magunguna ta NAFDAC da ta taba gargadar masu sayar da kayan marmari da su guji amfani da allurai ko hoda wajen nunar da kayan marmari saboda illar su ga lafiyar mutane.

Sakamakon bincike:

Bisa bayanan hukumar bunkasa fasahar halittu ta Najeriya da sauran hukumomin kula da abinci na nuna cewa ana samar da kayan marmari na GMO ne ta sauya ko sanya kwayar halitta a iri ba wai bayan sun fito ba.
Wannan dalili yasa kafar tantance labarai, bincike da bindiddigi ta Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari na cewa an yiwa agwaluma allura domin zama GMO a matsayin karya ne.
Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

  Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da...

Najeriya-Saudiyya sun karyata labarin cewa za’a hana ‘yan kasar bizar shiga Saudiyya

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta karyata ikirarin karya da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda ke cewa...

Ina gaskiyar cewa Amurka, Faransa ke neman haddasa faɗa tsakanin Sudan da Chadi?

  Duk lokacin da aka sami wata hatsaniya ko rikici tsakanin kasashe, wasu na amfani da wannan dama wajen yada...

Bidiyon ƴan sanda sunyi kame a Edo ƙarya ne, bidiyon ya faru a Ghana ne

  A yayin da ƴan Najeriya ke cigaba da Allah wadai da kisan wasu matafiya a jihar Edo, wasu na...

Karanta wannan

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar