Akwai dai ikirari dake matuƙar yaɗuwa a kafafen sada zumunta dake da alaƙa da sabon hafsan sojojin ruwa na Najeriya Rear Admiral Idi Abbas.
Iƙirari:
Wasu shafukan sada zumunta na facebook, X wato twitter, da whatsapp sun yaɗa labarin cewa sabon hafsan sojan Ruwan Najeriya Rear Admiral Idi Abbas haifaffen garin Jos ne kuma ya taba fuskantar kabilanci kan samun takardar shaidar zama dan jihar filato.
Misali wani shafin Facebook mai suna Rariya Online ya wallafa cewa “Dan Jos da aka hana shaidar dan kasa ya zama ya zama shugaban sojojin ruwan Najeriya.

Wani shafin mai suna Datti Assalafy shima ya wallafa labarin.

Wannan shafin da wannan da sauran su duk sun wallafa wannan labarin.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba CV din Rear admiral Idi Abbas wanda ya fito daga fadar shugaban kasa inda ya tabbatar da cewa, an haifi Abbas a jihar Kano kuma yayi makarantar Firamare a Gwagwarwa dake jihar Kano, sannan yayi makarantar sakadanre ta sojan sama a garin Jos.

Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta binciki bayanan inda aka haifi Rear Admiral idi Abbas inda aka tabbatar mata cewa a jihar Kano aka haife shi, kamar yadda anan aka haifi ‘yan uwansa ciki har da ɗan uwansa uwa ɗaya uba ɗaya wanda ya rasu.
Haka zalika binciken Alkalanci ya gano cewa akwai ƙanin sabon hafsan sojan ruwan dake sana’ar tuƙa babbar mota a garin na Jos wanda yana zuwa Kano sosai.
Sannan binciken kafar tantance labarai ta Alkalanci ta bakin wasu ‘yan uwan sa na jini da makwabta a jihar Kano sun musanta wancan iƙirari inda suka ce a Kano aka haifeshi kuma karatu kaɗai ne ya kaishi Jos.
Sakamakon bincike:
Bisa samun CV din Rear Admiral Idi Abbas daga fadar shugaban kasa da kuma shalkwatar sojin ruwan Najeriya dake nuna cewa an haife shi a Kano ne, kuma yayi firamare a Kano. Sai kuma musanta cewa an haifeshi a Jos da ‘yan uwansa da makwabta sukayi ya sanya Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan labarin dake yaduwa kan Rear admiral Idi Abbas na cewa an haifeshi a Jos kuma ya nemi shaidar zama dan jahar amma bai samu ba ƙarya ne.

Madalla