Fayyace abubuwaRaba zare da abawa: Mulkin Kyaftin Ibrahim Traoré da...

Raba zare da abawa: Mulkin Kyaftin Ibrahim Traoré da makomar Burkina Faso

-

Tun bayan da Kyaftin Ibrahim Traoré na rundunar sojojin Burkina Faso ya ɗare bisa karagar mulkin ƙasar bayan ya hamɓarar da gwamnatin Shugaba Paul-Henri Sandaogo Damiba a watan Satumban 2022, sannu a hankali ya shiga zukatan al’umomin nahiyar Afirka, har ma da mutane masu kishin ƴantar da jama’ar Afirka daga hannun turawa ƴan mulkin mallaka, musamman daga Yammacin Turai.

An haifi Ibrahim Traoré ne ranar 14 ga watan Maris na shekarar 1988. Shekarunsa 37 da haihuwa.

Ganin ƙarancin shekarunsa (shi ne shugaba mafi ƙarancin shekaru tsakanin dukkan shugabannin Afirka a yanzu), da salon mulkinsa na ɗaukan matakin warware matsaloli take-yanke, sai mutane suka fara sa rai cewa da alama an yi sa’ar samun shugaba mai kishin ƙasarsa da al’ummarsa.

Ya kuma ɗora tsarin mulkinsa bisa tafarkin marigayi Thomas Sankara – wanda makusancinsa Blaise Compaoré yayi masa kisan gilla kuma ya maye gurbinsa a muƙamin shugaban Burkina Faso – lamarin da ke tafasa zuciyar dukkan masoyin ci-gaba da samar da ƴanci.

Kyaftin Traoré ya riƙa furta kalamai masu ƙarfafa gwiwar ƴan ƙasarsa – har ma da sauran mutane masu kishin ƙasa a sauran sassan duniya.

Ya kuma ɗauki matakai na ƙwato kadarorin ƙasarsa daga hannun tsohuwar uwar ɗakinsu Faransa.

Ya kuma kori sojojinta da sauran kamfanonin da ta kafa domin hakar ma’adanai da Burkina Faso ke da su kamar zinare.

Daga baya, ya yanke dukkan wata hulɗa da ƙasashen yammacin Turai sannu a hankali. Wannan mataki ya sa Ibrahim Traoré ya zama abin da a Turanci ake kira “target” ga makiyansa, inda a ɗaya ɓangare ya zama “gwarzo” ga masoyansa.

Ana iya cewa a halin yanzu, babu shugaba mai farin jini irinsa a nahiyar Afirka. Lamarin da yasa wasu shugabannin ke fuskantar matsin lamba daga al’umominsu, na su ma su ɗauki salon mulkin nasa.

Halin da Burkina Faso ke ciki

Babbar tambaya a nan ita ce, “Shin a wane hali Burkina Faso ke ciki bayan shekara biyu na mulkin Kyaftin Ibrahim Traoré?

Masu bibiyar shafukan sada zumunta dai sun sha ganin bidiyo barkatai da ake haɗawa ta hanyar amfani da Ƙirƙirarriyar Basira (AI) da ke ƙoƙarin nuna bajintar wannan shugaba.

To domin gano inda ƙasar ta nufa, da kuma kawar da jita-jita, ɗan jarida Mo Sani Aliyu – wanda wakilin tashar talabijin ta Channels ne mai kula da yankin Sahel, ya yi tattaki zuwa Burkina Faso, inda a halin yanzu ya zagaya zuwa manyan garuruwa da ƙananan ƙauyukan ƙasar, musamman a yankin tsakiya da na kudu, da kuma yammacin ƙasar domin gane ma idonsa ainihin gaskiyar lamarin.

_”Na san abin da zan faɗi a yau ba zai faranta ran yawancin masu bibiyar abin da ke faruwa a Burkina Faso ba. Sai dai ita gaskiya ɗaya ce. Aikina na ɗan jarida mai ƙwarewa ta shekaru masu yawa, ta sa tilas in faɗa muku ainihin abin da ke wakana, ko da kuwa zan yi baƙin jini.”_

*Mo Sani Aliyu* .

Da farko, yawancin bidiyon da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta – waɗanda ke nuna cewa Kyaftin Ibrahim Traoré na kawo gagarumin sauyi a ƙasar – a gaskiya labarai na ƙanzon kurege ne ake danganta wa ga shugaban. Yawanci ma da Ƙirƙirarriyar Basira (AI) aka haɗa irin waɗannan tarin bidiyon. A kan fassara kalamansa da AI domin jan hankulan mutane cewa shi ne ke faɗin kalaman, misali da harshen Turanci.

Yawancin batun ayyukan ci-gaba da ake cewa Kyaftin Ibrahim Traoré ya ƙaddamar a ƙasar ba gaskiya ne ba. Waɗannan sun hada da cewa wai, Burkina Faso ya fara ƙera jiragen sama da motoci masu aiki da lantarki da ma samar da butum-butumi (robots) domin yaƙar ƙasashen da ke adawa da mulkinsa.

Yana dai koƙarin farfaɗo da tsofaffin kamfanoni da suka daɗe a rufe. Akwai kamfanin Coca-Cola da na jirgin sama na ƙasar, wadanda sun dawo bakin aiki, amma jirgi ɗaya tilo kamfanin jirgin sama na ƙasar ke da shi kawo yanzu.

Babu wani kamfanin ƙera motoci masu aiki da lantarki ko na ƙera jirgin sama ko kamfanonin da ke samar da fasahar AI a faɗin ƙasar.

Wannan al’amari ne wanda duk wanda ke so ya sani, zai iya shiga mota daga Najeriya ko Nijar ko Ghana ko ma Chadi da Kamaru zuwa nan domin ya tabbatar.

A gaskiya, yawancin ƴan ƙasar manoma ne da masu yin ƙananan sana’o’i.

Kamar yadda wani malamin jami’a a Ouagadougou ya shaida min, za a iya shafe shekara 20 kafin ƙasar ta fara girbar ayyukan da wannan gwamnatin ke yi a yanzu.

Ƙasar tana fama da matsaloli na rashin tsaro a arewaci da yammacin ƙasar, inda ƴan ta’adda suka ƙwace yankuna masu yawa kuma suka tarwatsa mazauna yankunan.

A halin yanzu ma, dubban ƴan ƙasar ma na gudun hijira a Ouagadougoubda birane da ke kudancin ƙasar.

Akwai talauci da rashin ayyukan yi, musamman ga matasa. Rashin ci gaba a fagen tattalin arziki da ƙarancin masana’antu babbar matsala ce. Fiye da shekara 50 ƙasashen Turai ne ke gudanar da ɓangaren haƙo ma’adinai irinsu zinare na ƙasar.

Sai a bana wannan gwamnatin ta ƙwato masana’antun kuma zai ɗauki shekaru kafin a fara cin gajiyar sashen.

Akwai kuma wani mataki da gwamnatin mai ci ta ɗauka na miƙa batun tsaro da na tattalin arziki kacokan ga kasar Rasha. A ganina, yin haka tamkar sauya wani uban gida ne (Faransa) da wani irinsa (Rasha).

Babu tabbacin matakin zai haifar da sakamakon da ake so, domin da ma’adanai Burkina Faso ke biyan Rasha domin ta samar da tsaro da kuma kariya daga ƙasashen Yamma.

_Kashi na biyu na wannan rahoton yana tafe._

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar