Hukunci: Ƙarya ne
Bisa bayanan kwamandan hukumar kare haddura dake kula da Abuja Chorrie Mutu’a inda ya tabbatar wa Alkalanci mutane uku ne suka mutu. Sannan bayanin dan jarida Abbas Dalibi da abin ya faru a gaban idonsa yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin da ake yadawa na mutane sama da 100 sun mutu a hadarin mota a hanyar Abuja zuwa Lokoja karya ne.
Ikirari:
Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa wani labari tare da hotuna wanda ya yadu matuka da yake ikirarin cewa mutane sama da 100 sun rasa ransu a hadarin mota a hanyar Abuja zuwa Lokoja.
“ INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIL RAJI’UN
Haɗari Mota Mai Muni Kan Hanyar Abuja Zuwa Kaduna Kusan Mutum 100 Sun Rasu.
Yanzu Muke Samu Rahoton Wani Mummunan Hadari Ya Faru Inda Wata Mota Tayi taho mugama da Babbar Motar daukar Shanu a Kan hanyar Kaduna Zuwa Abuja Birnin Tarayyar Najeriya.
Ana hasashen mutune kusa 100+ sun mutu, Da kuma Shanu Masu yawa da suka mutu.
Allah Ya Jikan Waɗanda Suka Rasu Masu Raunuka Allah Ya basu Lafiya Ameen
~Karaduwa Post

Wani shafin na Facebook mai suna Karamchi shima ya wallafa wannan labari.

Wani shafin na Facebook mai suna Hausa plus shima ya wallafa wannan labari.

Bincike:
Kafar tantance labarai bin diddigi da bincike ta Alkalanci ta tuntubi kwamandan hukumar kare haddura ta Najeriya dake kula da Abuja Muta’a Chorrie inda ya bayyanawa Alkalanci cewa mutane uku ne suka kone kurmus a hadarin da ya faru yau Juma’a 18/04/2024. Haka zalika mutane 25 ne hadarin ya rutsa da su, mutane 11 suka sami raunika inda ka kai su zuwa asibitin Kwali.
Ya bayyana cewa hadarin ya faru ne da misalin karfe 10:05am na safe kuma jami’an kare haddura dake yankin na Gada biyu (‘Yan Goje) suka sami kira da misalin karfe 10:07am suka kuma isa gurin da hadarin ya faru da misalin karfe 10:13am.
Bayanin na jami’in na hukumar kare haddura yace hatsarin ya faru ne tsakanin mota kirar Toyota Bas da kuma babbar mota da ake kira tirela (Howo-Sino).
Har ila yau Alkalanci ta tuntubi Abbas Dalibi babban editan wata kafar jarida mai suna AID Multimedia inda ya shaida faruwar lamarin domin anyi hatsarin dai-dai da yana wuce inda yayi Facebook live kuma binciken da yayi ya tabbatar da cewa direban babbar motar da yaransa da ma mutanen da suka biyo shanun da ya dauko sun tsallake rijiya da baya, yayin da direban motar Bus da ke dauke da kayan ya mutu a hatsarin. Ya kuma tabbatar da cewa adadin mutanen da suka mutu basu kai ko kusa da 100 ba.
Sakamakon Bincike:
Bisa bayanan kwamandan hukumar kula da haddura dake kula da Abuja na cewa mutum uku ne suka mutu ta hanyar konewa kurmus da kuma bayanin dan jarida da abin ya faru a gaban idon sa ya sanya kafar tantance labarai ta Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan labari da ake yadawa na cewa sama da mutane 100 sun mutu karya ne.