Hotunan mazaje da ake yadawa dai ba sune mijin Rahama Sadau ba hasalima binciken Alkalanci ya gano cewa wani daga ciki hotunan yana tare da ita sunanshi Comr Mahmud Muhammad. Ma’ana dai ‘yan social media sun canza masa suna zuwa Ibrahim Garba kuma sun daura masa aure da Rahama Sadau. Wani kuma abokin aikin ta ne mai suna Saleh Bala. Wani kuma hadin kirkirarriyar basirar AI ne.
Tun bayan bullar labarin auren shahararriyar ‘yar wasan kwaikwayo Rahama Sadau da wani mai suna Ibrahim Garba, hotuna ke cigaba da karade shafukan sada zumunta ana cewa ga hoton shi.
To sai dai kafar tantance labarai ta Alkalanci ta bi diddigi hotunan da ake cigaba da yadawa in da ta gano wasu bayanai da zasu baiwa masu karatu mamaki.
Da farko dai wasu sun yada wannan hoto a matsayin mijin Rahama Sadau.
Hoton karya da ake cewa shine mijin Rahama Sadau dake cigab da yaduwa
((https://www.facebook.com/share/p/14Fg7Arez98/?mibextid=wwXIfr))
To sai dai da Alkalanci tayi amfani da manhajar duba hoto na kirkirarriyar basirar AI ta gano cewa an hada mutumin da ita ne. Haka zalika an gano cewa anyi amfani da hoton Rahama Sadau data dauka a shekarar 2019 tare da abokin aikinta wajen hada wannan hoton dake cigaba da yaduwa a matsayin mijinta.
Hoton abokin aiki Rahama Sadau mai suna Saleh Bala da ake yadawa cewa shine mijinta
To amma akasin haka sunan shi Saleh Bala kuma daya daga cikin abokan aikin tane a gurin aiki.
Na hudu kuma wasu sun wallafa wannan hotun inda suke ikirarin cewa mijin Rahama Sadau ne.
Hoton karya da ake cewa shine mijin Rahama Sadau dake cigab da yaduwa
((https://www.facebook.com/share/p/1C5SsMDFzY/?))
To sai dai binciken Alkalanci ya gano cewa wanda ke tare da ita a hoton sunanshi Comr Mahmud Muhammad wanda tuni ya taya Rahama Sadau murnar aure. Ma’ana dai ‘yan social media sun canza masa suna zuwa Ibrahim Garba kuma sun daura masa aure da Rahama Sadau.
Kokarin mutane na samun likes da shares da kuma na mutane dake son ganin waye mijin shararriyar ‘yar fim din shine yasa wasu yada wadannan hotuna karya wanda wasu sun sami likes da comments dubunnai.