Galahanga dai shi ne haifar yaro da wasu ƙarin kwayoyin halitta. Yanayin kwayoyin halittar yawanci na shafar koyon wani abu da zai yi da kuma yanayin jikinsa.
Galahanga ko Autism a turance, wasu masana na cewa matsala ce ta shafi kwakwalwa da ke shafar yadda mutum yake fahimta, sadarwa, da hulda da wasu mutane.
Lalurar ba cuta ba ce, fyace rashin lafiya ko yanayin da wani zai iya kamuwa da shi. Ba a dai san me yake haddasa lalurar ba, domin kuwa haifar mutum ake yi da ita.
Ana samun waɗanda ake haifa da lalurar ko’ina a faɗin duniya kuma galibi tana yin tasiri a kan salon koyo, halayen jiki da kuma lafiya, a cewar hukumar lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ana haifar jariri ɗaya cikin 800 da galahanga, a cewar wani rahoto.
Alamomin autism sun hada da Matsaloli wajen sadarwa (irin su rashin iya magana ko fahimtar magana da kyau). Rashin iya yin hulda na zamantakewa yadda ya kamata (kamar rashin son kallon ido, rashin sha’awar yin abota ,yawan maimaita wasu motsi kamar girgiza hannu dade sauransu.
Duk da cewa Ba a san ainihin musabbabin autism kai tsaye ba amma wasu masana sun ce yana da nasaba da hadakar abubuwa na gado (genetics) da muhalli.
A halin yanzu dai babu maganin lalurar.
To amma ana iya ba da taimako bisa la’akari da buƙatun kowanne mutum me wannan lalura.
Wata Yar Amurka data bude makarantar koyar da yara masu fama da wannan lalura a Kano Laura Sharpe tace a Arewacin Najeriya mutane na alakanta wannan lalura da aljanu alhalin ba hakan bane.
Laura ta bayyana cewa Samun isassun hanyoyin kula da lafiya, shirye-shiryen bayar da taimako, ilimi, da kuma hakuri, na da muhimmanci wajen walwalar yara masu wannan lalura.

Ita kuma majalisar dinkin duniya ta ce za a iya inganta rayuwar mutanen da ke fama da galahanga ta hanyar biya musu buƙatu na lafiya.
Wannan ya kunshi gwaje-gwaje na yau da kullum tare da sa ido na ƙwararrun kiwon lafiya don duba yanayin tunani da jiki da kuma samar da lokaci mai mahimmanci kuma ilimi na musamman.
Wannan yana sauƙaƙe yanayin mu’amalarsu a cikin al’umma da kuma biyan buƙatun kansu.
Yawancin wanda mutane ke ganewa itace wacce tayi tsanani yayin da akwai masu fama da wannan lalura birjik ba tare da sun san lalurar bace.
wannan yasa ba kamar yadda wasu ke alakanta lalurar da iskokai ba, lalura ce da ake haifar mutum da ita kuma Idan ya sami kulawa yana iya zama mutum mai hazaka da kaifin basira.
