A wani bidiyo da ya yaɗu matuka anga wani sojan RSF a Sudan yana murmushi yayin wasu ke roƙon da kada a kashe su, to amma sakanni kaɗan aka harbe su.
An bayyana sunan wannan sojan da Abu Lulu. Bidiyon wannan kisa dai sashen tantance labarai na BBC mai suna BBC Verify sun tabbatar da ingancin sa. Sun kuma bayyana cewa wasu bidiyoyin da dama sun tabbata da cewa dakarun RSF sun kasha fararen hula.
Ta dalilin harin da dakarun RSF suka kai a El-Fasher dake yankin Darfur a ƙasar Sudan ya janyo hankulan duniya kan irin zub da jini da ake yi a ƙasar da yanzu ta rabu gida biyu.
An sha zargin Abu Lulu da kisan gilla ga fararen hula.
Tuni dai shugaban dakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo ya bada umarnin ka ma Abu Lulu wanda yanzu yake fuskantar bincike.
Waɗanne Ƙasashe ake zargi da hannu wajen yaƙin Sudan?
Tunda da aka fara wannan yaƙi dai tsakanin dakarun sojin ƙasar ta Sudan karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da shugaban dakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo ake zargin wasu ƙasashe da hannu a ciki.
Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE
Cikin binciken dake alaƙanta UAE da wannan rikici na goyon bayan RSF akwai wanda gidan jarida na Aljazeera yayi dake nuna cewa, akwai sojojin haya daga kasar Colombia sama 300 da wani kamfanin tsaro dake UAE ya ɗauka kuma ya tura zuwa Sudan suna yaƙi tare da dakarun RSF.
Gidan jaridar Sky News cikin hirar sa da wasu manyan dakarun RSF sunce ƙasar ta UAE ce ke ɗaukar nauyin RSF.
Wakilin ƙasar ta UAE a majalisar Dinkin Duniya Mohamed Abushahab ya musanta wannan ikirari na cewa ƙasar sa ce take rura wutar rikicin Sudan ta hanyar goyon bayan RSF.
Ƙasar Rasha
Binciken gidan jaridar Sky News shi kuma ya nuna cewa ƙasar Rasha na da hannu dumu-dumu wajen rura wutar rikicin ƙasar ta Sudan, domin an sami sojojin hayar Wagner group suna aiki a kasar a farko-farkon yaƙin.
Kwanakin baya ma dai akwai wani bidiyo da wani babba malamin addini ya sanya a shafin sa wanda aka ga wani jirgi mai saukar ungulu ya sauka a wani fili wasu fararen fata na sakkowa inda yayi iƙirarin cewa turawa ne ke baiwa ƴan ta’adda makamai.
To sai dai bayan tantance bidiyion Alkalanci ta gano cewa a kasar Sudan ne aka ɗauki wannan bidiyo.
Mai sharhi da kawo rahoton tsaro mai suna Zagazola Makama ya bincike bidiyon inda ya gano cewa jirgin ƙirar kasar Rashe ne kuma fararen fatar ma turawan Rasha ne.
Binciken ƙasa da ƙasa dai ya sha bankaɗo tare da nuna yadda sojojin hayar na Rasha a ƙasashen Afirka da aikata kisan gilla da take haƙƙin bil’adama.
A kwanakin baya ma dai wani binciken gidan jaridar Daily Trust ya nuna cewa akwai gwal ɗin Zamfara na zuwa Dubai na ƙasar ta UAE.
