Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun tsohon bidiyo na shekaru huɗu da suka gabata da Shaikh Ibrahim Daurawa yayi waɗancan kalamai kan Abduljabbar ba Triumph ba. Sannan an kasa samun inda yayi wani sabon bayani makamancin hakan a wannan lokaci. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin da aka alaƙanta da Shaikh Ibrahim Daurawa na cewa ya faɗa akan Lawal Triumph ƙarya ne.
Yayin da ake cigaba da taƙadda kan batun Malam Lawal Triumph a jihar Kano kan batun daya shafi addini. Akwai dai iƙiraran ƙarya dake yaɗuwa matuƙa a kafafen sada zumunta.
Iƙirari:
Akwai wani shafin Facebook mai suna Kano Update News ya wallafa wani iƙirari a ranar 6/10/2025 inda ya wallafa wani bayani tare da alaƙanta shi da cewa maganar Shaikh Ibrahim Daurawa ce inda yake cewa;
“Bana goyon baya ayi muƙabala da lawan triumph, dalili na farko Ni ban yarda da hankalin wanda za’ayi muqabala dashi ba, ita muƙabala ana yinta ne da mai hankali, saboda in kaji maganganun kasan mai hankali bazai iya kwatantasu ga Annabinmu mai tsarki ba ku, ko da maƙiyi,
yanzu acikin littafin ashafa Alkadi iyyak, yana kawo maganganun wanda suka gayawa Annabi mummunar Magana, sai “yace bazan iya faɗar lafazin da suka faɗa ba, Saboda ina jin nauyi hakaito lafazin in jinginashi ga Annabi s.a.w.”

Cikin awannin biyar da wallafa wannan iƙirarin mutane sama da ɗari uku suka sharing, mutane da dama kuma suka tofa albarkacin baki wato comments.
Wani shafin na Facebook mai suna Arewa 28 shima ya wallafa wannan iƙirarin.

Bincike:
Binciken Alkalanci ya gano wani bidiyo da aka wallafa a ranar 27/2/2021 inda Shaikh Ibrahim Daurawa yayi magana kan muƙabala da Abduljabbar inda a nan ne ya fadi kalaman cewa bai yarda da hankalin Abduljabbar ba.
A dai wannan bidiyo da aka wallafa shekaru huɗu da watanni da suka wuce anan ne Shaikh Ibrahim Daurawa yayi waɗancan maganganu da yanzu aka dawo dasu ake cewa ya faɗa kan Malam Lawal Triumph.
Alkalanci ta bincika domin samun wani sabon faifan sauti na audio ko na bidiyo domin tabbatar da wannan bayani amma babu shi.
Haka zalika babu wata sahihiyar kafar jarida ko kafar yaɗa maganganun malamai data rawaito ko wallafa wannan iƙirarin a matsayin sabo ko kuma akan Lawal Triumph ne.
Sakamakon bincike:
Bisa samun tsohon bidiyo na shekaru huɗu da suka gabata da Shaikh Ibrahim Daurawa yayi waɗancan kalamai kan Abduljabbar ba Triumph ba. Sannan an kasa samun inda yayi wani sabon bayani makamancin hakan a wannan lokaci. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin da aka alaƙanta da Shaikh Ibrahim Daurawa na cewa ya faɗa akan Lawal Triumph ƙarya ne.
