Hukunci: Ƙarya ne
La'akari da kasa samun wannan labari a sahihan kafafen yaɗa labarai, ƙaryata wannan labari da shalkwatar rundunar sojin ƙasa tayi bayan Alkalanci ta tuntubi mai magana da yawun rundunar, tare da tabbacin cewa shugaban bai faɗi iƙirarin tilasta matasa shiga soji ba yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin dake yaɗuwa na cewa shugaban rundunar sojin ƙasa ta Najeriya yace idan matasa suka ƙi shiga aikin, za a tilasta su ƙarya ne.
Akwai wani iƙirari dake yaɗuwa a kafafen sada zumunta mataƙa kan hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftanal Janar Waidi Shaibu.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna Muhammad T Shehu ya wallafa iƙirarin cewa; “Shugaban Hafsan sojin Najeriya yace idan matasa sun ƙi shiga aikin, zasu wajabta wa duk wanda ya haura shekaru 18+ shiga aikin sojan….

Wanna wallafa ta sami shares da comments da dama.
Wani shafin Facebook mai suna Wakiliya shima ya wallafa irin wannan iƙirarin.
A shafin na Wakiliya dubban mutane sun tofa albarkacin bakinsu wasu kuma sun ƙara wallafawa wato shares.

Bincike:
Najeriya dai na fama da matsalar tsaro wanda hukumomin tsaron ke ƙoƙarin ƙara yawan dakaru.
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta turawa mai magana da yawun shalkwatar sojin Najeriya Laftanal Kanal Anele inda tace labarin ƙarya ne kuma abu ne da bazai iya faruwa ba.
Sannan Alkalanci ta tuntuɓi ƴan jaridar dake kawo rahoton tsaro da kuma labaran dake da alaƙa da soji inda suka tabbatar da cewa basu sami wani labarin manema labarai ko jawabi daga bakin shugaban sojin ƙasa na Najeriya.
Har ila yau Alkalanci ta gano cewa shugaban sojan ƙasa na Najeriya ya bayyana aniyar ɗaukar ƙarin sojoji 24,000. Ya faɗi hakan ne a ranar Laraba 19-11-2025 a Kaduna. Da Alkalanci ta tuntuɓi ƴan jaridar dake Kaduna sun bayyana cewa baya ga batun ɗaukar ƙarin soji shugaban rundunar soji bai faɗi batun tilasta matasa shiga soji ba.
Alkalanci ta ƙara da duba kundin tsarin mulkin Najeriya inda babu inda ya bayyana halascin tilasta wani ko wata shiga aikin soji.
Sakamakon bincike:
La’akari da kasa samun wannan labari a sahihan kafafen yaɗa labarai, ƙaryata wannan labari da shalkwatar rundunar sojin ƙasa tayi bayan Alkalanci ta tuntubi mai magana da yawun rundunar, tare da tabbacin cewa shugaban bai faɗi iƙirarin tilasta matasa shiga soji ba, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin dake yaɗuwa na cewa shugaban rundunar sojin ƙasa ta Najeriya yace idan matasa suka ƙi shiga aikin, za a tilasta su ƙarya ne.
