Akwai wani shafin Facebook mai suna CNB Hausa da ya wallafa ikirarin cewa “Wani Jirgin İran Dauke da Bam-Bamai Yayi Batan Hanya Ya Tinkaro Najeriya”
https://www.facebook.com/share/p/1By1gfWNUi/?
Bincike:
Kasar Iran dai ta kai harin ramuwar gayya kan Isra’ila tare da shan alwashin cigaba da yin hakan.
Tun bayan harin da Isra’ila ta kai Iran da yayi sanadiyyar mutuwar wasu manyan sojin kasar da kwararrun masana kimiyya sararin samaniyar kasashen ya kasance babu jirgin da ke sauka da tashi.
An dai tabbatar da hare-haren sama da na jirage marasa matuka tsakanin kasashen biyu.
Haka zalika babu wata sahihiyar kafar labarai da ta rawaito batan hanyar jirgin Iran.
Alkalanci ta duba shafukan hukumomin kasar ta Iran inda bata ga wani labari dake kama da wannan ikirari ba.
Sakamakon bincike:
Bisa kasa samun wani sahihin labari daga kafafen yada labarai ingantattu, da kuma shafukan hukumomin Iran ya sa Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan labarin cewa jirgin kasar Iran yayi batan hanya ya kamo hanya zuwa Najeriya karya ne.
