Tun bayan labaran barazanar shugaban Amurka na kaiwa Najeriya hari domin yakar ‘yan ta’adda, ake samun labaran karya, hotuna da bidiyon karya iri-iri.
Iƙirari:
A wani shafin Facebook mai suna ATV Hausa da wasu shafuka makamantansa; ciki har da Adamawa Rant HQ, an wallafa cewa:
“DA DUMI DUMI: Jim kaɗan bayan Ƙasar Amurka tace Zata kawowa Nigeria Hari Yanzu haka Gwamnatin Tarayya Zata rabawa Sojojin Najeriya sabbin motocin yaƙi, Za’a tura da wasu hanyar Kaduna zuwa Abuja, da jihar Borno da Katsina da Zamfara da Sauran jihohin Nigeria.”

Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba duk wasu shafuka da suka cancanta a ga wannan labari amma ba a samu sanarwa ko bayanin da ya tabbatar da wannan iƙirari ba.
Bayan bin diddin hotunan da Alkalanci ta yi kan hotunan da aka yi amfani da su a labarin, wanda da muka sanya daya daga cikin hoton a manhajar TinEye ta gano cewa hotunan ba su da alaƙa ta kusa ko ta nesa da abin da ake yaɗawa. Sakamakon ya nuna cewa hotunan sun fito ne daga wurare daban-daban kuma a shekaru mabambanta, wasu an wallafa su ne tun a shekarar 2023.
- Misali: wannan hoton:

Bayan wani bincike a kan ƙarin shafukan da suka yaɗa ikirarin (misali Adamawa Rant HQ) mun gano cewa rubutun kwafar sa aka yi kai tsaye daga wani shafin daban.
Sakamakon Bincike:
Bisa binciken da Alkalanci ta gudanar, babu wata sanarwa a hukumance daga fadar shugaban ƙasa ko ma’aikatar tsaro ta Najeriya kan batun rarraba sabbin motocin yaƙi, kamar yadda aka yi iƙirari a wasu shafukan na Facebook. Sannan, an yi amfani da tsofaffin hotunan da aka wallafa da daɗewa a wasu shafukan daban. Wannan ya sa Alkalanci ta yanke hukuncin cewa iƙirarin ƙarya ne.
