BindiddigiLabarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado...

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa la’akari da ƙaryata wannan labari da Sakataren yaɗa labaran Sarki Aminu Ado Bayero ya yi, tare da rashin samun wannan labari a sahihan kafafen yaɗa labarai, da kuma tabbacin cewa maganar tana gaban kotu, Alkalanci ta yanke hukuncin cewa iƙirarin da ke cewa Janar Christopher Musa mai ritaya ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ƙarya ne.


Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado da bangaren Sarki Muhammadu Sanusi.
Iƙirari:

Wani labari yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta Facebook, musamman daga wani shafi mai suna MALAM KHAN NEWS, wanda wasu shafukan suka yada, inda aka yi iƙirarin cewa Janar Christopher Musa, Ministan tsaron Najeriya, ya fitar da umarni mai cewa:

“Aminu Ado Bayero Yazo ya samini nan da awa 24 kuma shi kadai, Saboda shi ba SARKI ba ne a wojen mu.”

Wannan wallafa ta jawo cece-kuce tare da samun martani daga mutane da dama a shafukan sada zumunta, inda wasu ke ganin kamar gaskiya ne.

Bincike:

Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike kan wannan iƙirari domin gano gaskiyar lamarin.

Da farko, Alkalanci ta tuntuɓi Abubakar Balarabe Ƙofar Na’isa, Sakataren yaɗa labaran Sarki Aminu Ado Bayero, domin jin ta bakinsa. Ya tabbatar da cewa labarin ba gaskiya ba ne, inda ya ce:

“Mu ma haka muka tsinci labarin nan ana yaɗa shi, amma ba gaskiya ba ne. Magana tana gaban kotu, don haka ba a yanke hukunci ba har yanzu. Saboda haka wannan labarin ba gaskiya ba ne.”

Na biyu, Alkalanci ta gudanar da bincike a manyan kafafen watsa labarai na gida waɗanda aka sani da kawo sahihan labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya, amma babu ko ɗaya da ya rawaito wannan labari. A al’adance, umarni mai ƙarfi irin wannan daga babban jami’in tsaro kamar Christopher Musa zai kasance babban labari a jaridun ƙasa.

Na uku, salon yadda aka rubuta labarin a Facebook yana ɗauke da kurakurai da kuma kalaman da ba su dace da tsarin magana na manyan jami’an gwamnati ba.

Sakamakon Bincike:

Bisa rashin gamsasshiyar shaida ta labarin da ake yaɗawa, da rashin samunsa a sahihan gidajen jaridu, tare da bayanin ƙaryatawa daga bakin Sakataren yaɗa labaran Sarki Aminu Ado Bayero, Abubakar Balarabe Ƙofar Na’isa, Alkalanci ta tabbatar da cewa labarin ƙirƙirarre ne kuma ba shi da asali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Karanta wannan

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar