BindiddigiLabarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa rashin samun wata sanarwa daga ɓangarorin da abin ya shafa ko sahihan kafafen yaɗa labarai, tare da maganar Aisha Buhari tayi da kanta na cewa bazata kara aure ba yasa Alkalanci ta yanke hukuncin cewa iƙirarin da ke cewa tsohuwar matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta amince da auren Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ce da aka ƙirƙira don jawo hankalin jama'a.

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda suke basu da tushe.

Iƙirari:

Wani shafin Facebook mai suna “CLASSIC TV” ya wallafa wani labari mai taken: “DA ƊUMI ƊUMI: Aisha Buhari ta Amince da sheikh isah Ali Fantami Amatsayin wanda zata aura.”

Labarin karya da ya yadu

wasu shafukan ma sun wallafa wannan labari kamar wannan shafin da wannan ma.

Wannan labari yana ta yaɗuwa a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke ta tofa albarkacin bakinsu, duk da cewa babu wani cikakken bayani ko hujja da shafin ya gabatar.

Bincike:

Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike don gano gaskiyar lamarin:

1. Rashin Sahihan Majiya: Binciken da aka gudanar a manyan gidajen jaridu da kafafen yaɗa labarai masu inganci (kamar BBC Hausa, Daily Trust, da sauransu) ya nuna babu ko ɗaya da ya wallafa wannan labari. Idan da gaske ne cewa mata tsohon Shugaban Ƙasar da fitaccen Malamin addinin suna shirin aure, zai zama babban labari da kowace kafa za ta ɗauka.

2. Yanayin Shafin: Shafukan da suka wallafa labarin sunyi shahara wajen wallafa labaran da ba su da tushe domin samun yawan masu kallo da ‘comments’. Irin waɗannan shafuka sukan yi amfani da kanun labarai masu jawo hankali ba tare da bincike ba.

3. Rashin Sanarwa: Babu wata sanarwa daga ofishin Aisha Buhari ko daga Sheikh Isa Ali Pantami ko iyalansu da ta tabbatar da wannan batu. A irin waɗannan al’amura na aure tsakanin manyan mutane, akan sami sanarwa ko ishara daga majiyoyi ta kusa, amma a nan babu.

4. Aisha Buhari a ranar da aka kaddamar da litattafin tarihin marigayi Muhammadu Buhari ta ce ba zata kara yin aure ba, guda daya da tayi ya isa.

Sakamakon Bincike:

Bisa la’akari da cewa labarin ya samo asali ne kawai daga shafukan da ba su da sahihanci, kuma babu wata sahihiyar kafa da ta tabbatar da shi, Alkalanci ta tabbatar da cewa labarin ƙarya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Wasu shafukan da suka dinga yaɗa ƙage da labaran ƙarya a shekarar 2025

Shekarar 2025 dai ta kasance shekarar da aka sami wasu shafukan sada zumunta da kaso mafi yawa na abubuwan...

Karanta wannan

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar