BindiddigiLabaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

-

 

Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da kasar Burkina Faso, tun bayan juyin mulkin da Ibrahim Treore yayi a kasar.

Duk da kasancewar kasar ta Burkina Faso kasace da ake amfanin da harshen Faransanci a harkokin gwamnati to amma abun daure kai shine wadannan labarai dake fitowa daga kasar dake yaduwa kamar wutar daji a shafukan sada zumuntar Najeriya kan kasance cikin harshen turancin Ingilishi wasu lokutan kuma Hausa.

Wani Shafin TikTok mai suna Africa Mail TV dai na cikin manyan shafukan dake yada labarai dangane da kasar Burkina Faso a harshen turanci. Wadannan labarai mafi akasarin su na karya ne.

Hoton shafin dake yada labaran karya

labarin gina gidaje kyauta ga duk ‘yan kasa

Labarin cewa shugaban kasar ta Burkina Faso na gina gidaje kyauta ga ‘yan kasar ya sami mutane sama da miliyan daya da suka kalli bidiyon da aka wallafa a Shafin na Africa Mail TV wanda kuma karya ne domin bidiyon gidajen da akai amfani dasu, anyi amfani da kirkirarrayar basirar AI. ((https://vm.tiktok.com/ZMB9TFPHL/))

Hoton labarin karya na gina gidaje kyauta ga duk ‘yan Burkina Faso

Sannan wannan shafi ya wallafa wannan labari sau uku lokuta daban-daban wanda a wani anyi amfani da Hashtag Nigeria da sauran kasashe masu magana da turanci irin su Ghana, Kenya da Afrika ta kudu.

Hoton labarin karya

Har ila yau Shafin ya wallafa wannan bidiyo tare da ikirarin cewa shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci ministocinsa da su duba yadda Burkina faso keyi na samar da gidaje kyauta ga ‘yan kasar wanda ya kasance labarin karya. Babu inda shugaban Najeriya ya bukaci hakan. ((https://vm.tiktok.com/ZMB9TBprE/))

Hoton labarin karya

Wasu shafukan wanda ya hada da wani mai suna Truth Unvailed ((https://vm.tiktok.com/ZMBxFb2FG/)) da ZD Mother of all nations ((https://vm.tiktok.com/ZMB9wrrJU/)) sun wallafa labarin da ma bidiyon gidajen da ake a kasar Algeria tare da ikirarin cewa su ake ginawa a Burkina Faso kyauta ga ‘yan kasar. Wadannan sun shahara wajen yada labarai na Burkina Faso domin ‘yan Najeria wanda galibin labaran karya ne.

Hoton shafin dake yada labaran karya

Me yasa suke amfani da Ingilishi?

Haka zalika kafar tantance labarai, bin diddigi da bincike ta Alkalanci ta gano cewa akwai shufukan da dama dake yada irin wadannan labarai ta amfani da turanci kuma suna amfani da hashtag na Nigeria da wasu kasashe masu Magana da Ingilishi.

Wadannan shafuka dai sunyi shura wajen wallafa labaran da zasu janyo hankalin mutane tare da tunzura matasan kasashen dake magana da harshen turanci. Misali shafukan sun wallafa wani labari cewa shugaban na Burkina faso ya kalubalanci shugabannin Africa kan yadda sukai watsi da bukatarsa ta hada kan Afrika ta zama dunkulalliya, kuma su dinga shige da fice ba tare da biz aba. Wannan labarin karya ne. Domin kuwa babu wata sanarwa daga ma’aikatar kasar ta Burkina Faso dake nuna cewa ‘yan kasashen Afrika zasu shiga ba tare da biza ba hasalima kasar ta Burkina Faso ta kakabawa kasashen ECOWAS haraji duk wani kaya da zai shiga wanda ya sabawa kudirin cinikayya bai daya tsakanin kasashen Afrika. ((https://vm.tiktok.com/ZMB9Tf9Gd/))

Daliban Burkina Faso zasu sami CFA 100,000

Wani labari da ke kara yaduwa har ila yau a kafar ta Tiktok dama sauran kafafen sada zumunta, shine na cewa shugaban kasar ta Burkina Faso ya ayyana karatu kyauta tare da bayar da CFA 100,000 ga kowanne dalibin jami’a a kasar duk wata. Wannan labari ma na cigaba da yaduwa matuka a kafafen sada zumunta na Najeriya duk da cewa karya ne. Babu wani jawabi ko wata sanarwa daga hukumomin kasar ta Burkina Faso kan wannan labarai.

Sannan akwai labarin cewa kasar ta biya dukkan basusussukan da ake binta na ciki da waje, to sai dai alkaluman asusun bada lamuni na duniya dama bayanan ministan kudin kasar sunci karo da wannan labari. Wato dai wannan labari karya ne. ((https://vm.tiktok.com/ZMB9w15Rn/))

 

Su dai wadannan shafuffuka na amfani da labari daya ne suna yada shi, duk da cewa kasar ta Burkina Faso na fama da hare-haren ‘yan tada kayar baya wanda ko a kwanakin baya sojin kasar da dama sun mutu dalilin hari, to sai dai irin wadannan shafuka basu taba nuna ko kawo irin wannan labari ba.

A yanzu dai wasu kasashe na amfani da farfaganda da labaran karya domin sauya manufofi, tunzura matasa, dama batun zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Najeriya-Saudiyya sun karyata labarin cewa za’a hana ‘yan kasar bizar shiga Saudiyya

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta karyata ikirarin karya da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda ke cewa...

Ina gaskiyar cewa Amurka, Faransa ke neman haddasa faɗa tsakanin Sudan da Chadi?

  Duk lokacin da aka sami wata hatsaniya ko rikici tsakanin kasashe, wasu na amfani da wannan dama wajen yada...

Bidiyon ƴan sanda sunyi kame a Edo ƙarya ne, bidiyon ya faru a Ghana ne

  A yayin da ƴan Najeriya ke cigaba da Allah wadai da kisan wasu matafiya a jihar Edo, wasu na...

Waɗanne ƙasashe ne ke rura wutar yaƙin Sudan?

Yaƙin Sudan dai ana yin sane tsakanin dakarun sojin ƙasar wanda  Janar Abdul Fatah Al-Burhan ke shugabanta kuma shine...

Karanta wannan

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar