Iƙirarin dake yaduwa matuka a shafin TikTokinda yake cewa fitowar kurji a wani sashe na fuska na nuna alamar wata cuta a cikin mutum babu wani bincike na kimiyya da ya tabbatar da hakan, wanda yasa ikirarin ya zama na karya.
Iƙirari:
- Idan kaga pimple a goshin ka matsala ce ta narkewar abinci
- Idan kaga pimples a gira wannan matsala ce ta hanta (liver)
- Idan kana da kurji a hanci wannan matsala ce ta zuciya
- Sannan kurji kunne matsala ce ta koda wato kidney
- Kurji a baki matsala ce ta ciki.
- Kurji a kumatu matsala ce ta huhu.
- Kurji a gurin gemu wannan matsalce ta hormones
Bincike:
Kafar tantance labarai bindiddigi da bincike ta Alkalanci mun tuntubi wata likita a Abuja mai suna Dr. Hajar Mamman Nassir inda tace; Wadannan ikirari na taswirar fuska, abu ne dake cikin maganin gargajiyar na kasar Sin, tace akwai duk da cewa wani bangare na fuska na da alaka da batun lafiya to amma babu wani bincike da likitocin fata na zamani sukayi da ya tabbatar da cewa ganin wani kurji a wani sashe na fuska na nuna wata rashin lafiya.
- Ƙurji a goshi baya nuna cewa mutum na fama da matsalar narkewar abinci.
Domin kuwa ana alakanta goshi da wani sashe na jiki da ake kira T-Zone inda yawan man fata ke haddasa ƙuraje. Duka da cewa matsalar abinci misali yawan cin abinci da aka sarrafa, suga na iya kawo ƙuraje. To amma batun ƙurjin pimples na samuwa ne a yawancin lokuta ta dalilin rashin isasshen bacci, ayyuka da yawa wato stress da sauran su.
Don haka wannan ikirari karya ne. - Ƙurji a gira baya nuna matsalar hanta.’
Ana iya gani ko gane alamun hanta ne ta hanyar ganin fata da ido sun zama ruwan dorawa ko yawan gajiya ba wai ta hanyar ganin ƙurjin pimples ba. Ƙurji a gira na samuwa ne a yawancin lokuta saboda an cire gashi, kwalliya, ko gyaran gira. - Babu wata alaka dake tsakanin ƙurji a hanci da ciwon zuciya.
Yawancin lokuta ƙurji a hanci na faruwa ne saboda yawan man fata. - A binciken harkar lafiya babu wata alaka tsakanin ƙurjin kunne da ciwon koda wato kidney. Ana gane alamomin cutar koda ne ta hanyoyin, kunburin wasu sassan jiki, canjin kalar fitsari, yawan gajiya da sauransu. Ƙurji a kunne na samuwa ne saboda kwayar cuta daga samu saboda taba kunne, fuskar waya ko abun sautin kunne mai datti dake ɗauke da wasu kwayoyin cuta da kuma rashin daidaiton hormones.
- Kuraje ko kurjin Lebe ko baki a wasu lokuta na da alaka ta kusa ko ta nesa da ciwon ciki
Domin a wasu lokutan ana samun kurajen baki ne saboda matsalar abinci, matsalar cutar dake da alaka ciki.
To amma fa kurjin baki yafi faruwa ne ta dalilin amfani da wasu man fata, rashin daidaito na aikin hormone da kuma kwayoyin cuta na bacteria.
Wato dai shi wannan akwoi dan kam shin gaskiya. - Babu alaƙa ta kusa ko ta nesa tsakanin kurjin kumatu da cutar huhu
Kurjin huhu na samuwa ne ta dalilin hormones, kwalliya musamman ga mata, matashin kai mara tsafta ba wai cutar huhu ba. - Akwai ƙamshin gaskiya da kuma alaƙa tsakanin ƙuraje a gemu ko garin gashin baki da matsalar hormones.
Rashin daidaiton sinadarin hormones ga mata musamman lokacin al’ada na haddasa musu kuraje. To amma fa ga wasu aske ko saidaye gashin wurin wato shaving da kuma wasu kayan shafa wa fata na haddasa wannan matsala ta ƙurajen gemu da gurin gashin baki.
Sakamakon Bincike:
Bisa bayanan likita kan wadannan ikirari ya nuna cewa akwai alaka tsakanin wasu sassa na fuska da matsalar lafiya ta jikin mutum to sai dai da dama ba gaskiya bane.
Domin suna samuwa ne ta dalilan rashin daidaiton hormones, kwayar cuta, yanayin gudanar da rayuwar yau da kullum. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa na biyar da na bakwai ne ke da kamshin gaskiya yayin da sauran kuma ƙarya ne.