Fayyace abubuwaKo an baiwa Jeffrey Epstein kyautar rigar Ka’aba daga...

Ko an baiwa Jeffrey Epstein kyautar rigar Ka’aba daga Makka?

-

Rigar Ka’aba wato Kiswa dai abace  da musulmai da dama kan girmama ta saboda ta kasance rigar daki mafi tsarki ga musulman duniya, wanda ake sauyata a ranar Arfa wato 9 ga watan Zhulhijja kowacce shekara.
An dai sha rawaito cewa an baiwa shugabannin ƙasashen musulmai da manyan mutane  kyautar wani ɓangare na rigar kamar yadda majalisar ɗinkin duniya ta tabbatar.
Cikin tonon silili na kundin Epstein dai an ga wasu saƙwannin email dake nuna cewa an taɓa baiwa mutumin da aka taɓa ɗaurewa da laifukan fyade ga ƙananan yara da baɗala iri-iri kyautar rigar Ka’aba.
Epstein ya karbi rigar ta Ka’aba a watan Maris din shekarar 2017 a cewar sakon email. Bayan ya kammala zaman gidan yari bisa laifin fyade.
Sakon email ɗin dai yayi zargin cewa Epstein ya karɓi kyautar bangarori uku na rigar ta Ka’aba.
Jikin rigar ta ciki, jikin rigar ta waje da kuma wani ɓangare da ba ayi amfani da shi ba.
Samun rigar Ka’aba dai na da matukar wahala da tsada. Sakwannin Email ɗin sun nuna cewa an kaiwa Epstein rigar Ka’aba har gida ne.
Babu dai wani rubutaccen dalili na kaiwa mai baɗalar kyautar rigar ta Ka’aba. Wato takardun tonon sililin basu bayyana dalilan bashi rigar ba.
An dai sanya ɓangarorin rigar a matsayin kayayyin fasahar zane wanda yasa hukumomin kwastom na Amurka suka bar su suka shiga ƙasar.
Takardun dai sun nuna wasu mutane biyu mace da namiji masu suna Abdallah Al maari da Aziza Alahmadi dake gabas ta tsakiya sune suka tura rigar daga Saudiyya zuwa Florida.
Wannan tonon silili dai na bankaɗo wasu sirrikan manyan mutane masu kuɗi da mulkin a ɓangarorin duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Hoton magajin garin New York Zohran Mamdami cikin file ɗin lalata na Epstein haɗin AI ne

Kundin bayanai wato file ɗin lalata na Epstein na cigaba da haddasa maganganu iri-iri tsakanin mutane a faɗin duniya. Iƙirari: Akwai...

Hotunan Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna da ake yaɗawa tsofaffi ne

Tun bayan sauya sheƙar siyasa da Gwamnan Jihar Kano,  Abba Kabir Yusuf ya yi, ake ta yaɗa wasu hotuna...

Ko Benin, Ivory Coast da Faransa nada hannu wajen abinda ya faru a Yamai?

Bayan da aka sami harbe-harbe a filin sauka da tashin jiragen sama na Yamai babban birnin ƙasar Nijar, shugaban...

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta TikTok wanda ke nuna cewa jami'an tsaro sun kwashe...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Karanta wannan

Hoton magajin garin New York Zohran Mamdami cikin file ɗin lalata na Epstein haɗin AI ne

Kundin bayanai wato file ɗin lalata na Epstein na...

Hotunan Kwankwaso da Nasiru Yusuf Gawuna da ake yaɗawa tsofaffi ne

Tun bayan sauya sheƙar siyasa da Gwamnan Jihar Kano, ...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar