Isra’ila ta kashe wani shahararren ɗan jaridar kafar yaɗa labarai ta Aljazeera Anas Al-Sheriff da abokan aikin sa huɗu a Gaza.
Gidan talabijin na Aljazeera ya tabbatar da kisan ma’aikatan nata biyar, ma’aikatan Aljazeera sune; Anas Al-Sherif, Ibrahim Zaher, Mohammed Qreiqeh, Moamen Aliwa, Mohammed Naufal. An kuma tabbatar da mutuwar wani ɗan jarida mai zaman kansa a harin da Isra’ilan ta kai a tantin da suke zaune a kofar shiga asibitin Al-Shifah a Gaza.

A baya dai ƙasar ta Isra’ila ta zargi Anas da cewa yana shugabantar wani sashe na ƙungiyar Hamas wanda kafin rasuwarsa ya sha musanta hakan. Haka zalika gidan talabijin na Aljazeera shima ya musanta cewa Anas na da alaƙa da ƙungiyar Hamas.
“Anas na aiki ne kawai na kawo rahoto tare da bayyana irin ta’asar da Isra’ila ke aikatawa a Gaza, kuma ya zama muryar marasa murya” a cewa Editan gidan talabijin na Aljazeera.
Hukumar kare haƙƙin ƴan jaridu ta Duniya tace akalla ƴan jaridu 192 Isra’ila ta kashe tun fara sabuwar mamaya da kisan ƙare dangi da Isra’ila daga 7 ga watan Oktoba, 2023.
Gidan talabijin na Aljazeera shi kuma ya rawaito cewa ƴan jarida da ma’aikatan gidajen jaridu 270 ne suka mutu sanadiyar yaƙin tun daga ranar bakwai ga watan Oktoba 2023.
Cikin waɗannan ƴan jarida da Isra’ila ta kashe 269 Falasdinawa ne.

Majalisar ɗinkin Duniya tace wannan yaƙi ya zama wanda yafi muni kuma aka kashe ƴan jarida da yawa a tarihi.
Gidan jaridar BBC na Turanci ya buƙaci Isra’ila data bada shaidun cewa Anas jagora ne a ƙungiyar Hamas amma basu bayar ba, wanda yasa BBC ƙasa tabbatar da zargin ko akasin haka.
Wannan dai ba shine karo na farko da Isra’ila ke kashe ƴan jarida ba a Gaza.
