Makawakin siyasa a Najeriya Rarara ya kasance mutumin da ake ta ambata a shafukan sada zumunta tun bayan hirarsa da kafar DCL Hausa inda yayi magana kan rikicin shugabanin Najeriya da Nijar.
Batu:
Wani shafin Tiktok mai suna @abdou.salam.absi2 ya wallafa wani faifan bidiyo a ranar 5/1/2025 inda akaga mawakin nan Naziru sarkin waka kuma aka rubuta “New song by sarkin waka 🎶”

Wani shafin na Tiktok mai suna @binta56905 ya wallafa wannan (archived here) waka da bidiyo a ranar ta 5/1/2025.

Bincike:
Kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta tuntubi wani dan jarida dake aiki da gidan Talabijin na Arewa24 wanda ke gabatar da shirin fitattun wakoki Abubakar Habib Ibrahim inda yace; “ wannan ba Naziru Sarkin waka bane, domin duk da muryar ta danyi kama amma ba shi bane. Idan ka kula da kyau yanayin bakin Nazirun a wannan bidiyo bai hau wakar ba.”
Sannan kafar Alkalanci ta duba shafin Tiktok da Instagram na Naziru Sarkin waka amma bata sami wannan bidiyo ko wakar ba.
Sakamakon Bincike:
Bisa kasa samun wakar a shafukan Naziru Sarkin waka da kuma bayanin dan jarida mai gabatar da shiri dangane da wakoki Abubakar Habib Ibrahim yasa kafar bindiddigi ta Alkalanci ta yanke hukuncin cewa wannan iƙirari ƙarya ne.