Hukunci: Ƙarya ne
Bisa kasa samun labarin wannan daya nuna kifin ya kashe mai horas dashi mai suna Jessica daga sahihan kafafen yada labarai, kasa samun labarin a kowanne gandun killace namun ruwa wato Marine Park, sannan kasa samin gandun killace namun ruwa mai suna Pacific blue marine park da akawa rijista, sai kuma kasa samun wata mai horas da kifi mai suna Jessica. Da kuma gano cewa bidiyon da ake yadawa hadin kirkirarriyar basirar AI ne. Wannna yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin da bidiyon dake yaduwa na cewa kifi ya kashe mai horas dashi karya ne.
Wasu bidiyo dake kama da na gaskiya sun karade shafukan sada zumunta musamman shafin Tiktok inda bidiyon ke ikirarin cewa kifi jinsin Whale ya kashe mai horas dashi wacce ake kira Jessica Radcliffe.
Akwai dai bidiyo da dama dake bada wannan labari da kuma ikirari kala-kala.
Wasu bidiyon dake yawo a kafar sadarwa ta Tiktok da Facebook na ikirarin cewa dalilin daya sanya kifin kashe ta shine yayin da suke wasa inda yaji kamfshin jinin hailar ta ne.
An dai ga a bidiyon yadda wasu suka shiga cikin ruwan inda suka dakko wata mace jim kadan bayan ruwan ya dan canza launi zuwa ja.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta fara da duba ko akwai wata kafar labarai data rawaito wannan labari na kifin Whale ya kashe Jessica? To sai dai ba’a sami wata kafar jarida data rawaito wannan labari ba. Sannan bayan da Alkalanci ta duba shafin Marine Park babu wannnan labari na kisan Jessica ko batun shirye-shiryen jana’izar ta.
Haka zalika binciken Alkalanci bai sami wani Marine Park mai suna Pacific Blue Marine Park dake da rijista ba.
Sannan bincike ya nuna cewa kifin mai suna Tilikum ya taba kashe masu koyar dashi uku a tarihi.
Na farko ya faru a shekarar 1991, Ina ya kashe mai koyar dashi Keltie Byrne.
Na biyu kuma a shekarar 1999 inda kifin ya kashe mai horas dashi mai suna Daniel Duke.
Na uku kuma ya faru a shekarar 2010 inda kifi ya kashe mai horas dashi Dawn Brancheau, yayin wani wasa da suke a Orlando.
Na hudu kuma ya faru a shekarar 2009, inda kifin ya kashe mai horas dashi dan kasar Spain.
Binciken Alkalanci ya kuma kasa samo ita kanta Jessica Radcliffe mai horas da kifin wato dai bisa dukkan bayanai babu wata mai horas da kifi dake da wannan sunan.
Kafar Alkalanci tayi amfani da manhajar duba hotunan kirkirarriyar basirar AI inda sakamako ya bayyana cewa hadin AI ne. Haka zalika sautin bayanin dake cikin bidiyon shima yayi dai-dai da wanda ake yawan amfani dashi a bidiyo da akayi da AI.
Kafofin yada labarai irin su Economic Times ((https://m.economictimes.com/news/international/us/orca-attack-mystery-what-really-happened-to-marine-trainer-jessica-radcliffe/articleshow/123240619.cms) sun tabbatar da cewa wannan labarin hadin AI ne.
Sakamakon bincike:
Bisa kasa samun labarin wannan abu na ya kashe mai horas dashi daga sahihan kafafen yada labarai, kasa samun labarin a kowanne gandun killace namun ruwa wato Marine Park, sannan kasa samin gandun killace namun ruwa mai suna Pacific blue marine park da akawa rijista, sai kuma kasa samun wata mai horas da kifi mai suna Jessica. Da kuma gano cewa bidiyon da ake yadawa hadin kirkirarriyar basirar AI ne. Wannna yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin da bidiyon dake yaduwa na cewa kifi ya kashe mai horas dashi karya ne.
