Hukunci: Ƙarya ne
La'akari da cewa babu wannan labari ko hotuna a shafukan shugaban ƙasa, mai magana da yawun sa, da ma gidajen jaridu sahihai dake kawo rahoton da suka shafi wasanni, Sannan bisa la'akari da cewa babu inda aka rawaito shugaban Najeriya ya tarɓi tawagar ta Super Eagles bayan kammala gasar ta AFCON. Wannan ya sa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin da kuma hotunan dake cewa shugaba Tinubu ya baiwa Super Eagles gidaje da motoci ƙarya ne.
Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala dake yaɗuwa a kafafen sada zumunta.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna Muhammad Bala Hamisu ya wallafa wasu hotuna da kuma iƙirarin dake cewa; shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu Yabawa Yan Wasan Nigeria Kyautar Gidaje da Motoci da Kudi.

Bincike:
Alkalanci tayi amfani da Google search inda ta gano yadda wasu shafukan sada zumunta suka wallafa hotunan tare da iƙirarin da harshen turanci. Sai dai duk shafukan da suka wallafa labarin babu guda ɗaya da yake sahihi.
Haka zalika Alkalanci ta duba shafukan sada zumunta na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu inda ba a sami wannan labari ba. Sai binciken Alkalanci ya garzaya zuwa shafin Bayo Onanuga mai magana da yawun shugaban ƙasar Najeriya inda nan ma babu wannan labari.
Sannan Alkalanci ta ƙara da duba kafafen yaɗa labarai sahihai dake rawaito labaran wasanni amma babu wancan labari.
Gwamnatin Najeriya dai ta bakin ministan yaɗa labarai ta jinjina wa ƴan wasan na Super Eagles bayan da suka zo na uku a gasar, amma babu inda aka bayyana basu wata kyauta ta kuɗi, motoci ballantana gidaje.
Sakamakon bincike:
La’akari da cewa babu wannan labari ko hotuna a shafukan shugaban ƙasa, mai magana da yawun sa, da ma gidajen jaridu sahihai dake kawo rahoton da suka shafi wasanni, Sannan bisa la’akari da cewa babu inda aka rawaito shugaban Najeriya ya tarɓi tawagar ta Super Eagles bayan kammala gasar ta AFCON. Wannan ya sa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin da kuma hotunan dake cewa shugaba Tinubu ya baiwa Super Eagles gidaje da motoci ƙarya ne.
