BindiddigiIna gaskiyar cewa ‘yan ƙasar Iceland na azumin sama...

Ina gaskiyar cewa ‘yan ƙasar Iceland na azumin sama da awanni 22?

-

Hukunci: Ƙarya ne
A Azumin shekarar 1446AH/2025 tsawon awannin azumi a kasar ta Iceland daga farko har zuwa karshen azumi bazai wuce awanni 16 da mintuna 30 ba. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin dake cewa mutanen Iceland na Azumin sama da awanni 22 karya ne.

Duk shekara ana samun wasu ƙasashe sufi wasu tsawon lokacin shan ruwa. Yayin da wasu kanyi a yanayin zafi wasu kuma sanyi.

Iƙirari:

Akwai wani shafi Facebook mai suna Musa Abdullahi Sufi inda ya wallafa iƙirarin cewa ƴan ƙasar Iceland suna azumin awanni sama da 22 kafin su sha ruwa.
“Awa sama da 22 Suke Azumi: Kasar ICELAND da ke yankin turai itace kasa mafi tsawon awannin 22 na Azumi a 2025. A Kano Nigeria awa kusan 13 kawai muke amma wasu sai rakı.”
Ikirarin karya dake yaduwa.
Ikirarin karya dake yaduwa.

Bincike:

Kafar tantance labarai, bin diddigi da bincike ta Alkalanci ta gano cewa a iya bincike azumin wannan shekarar babu ida suke azumin awannin goma sha takwas ma balle awanni ashirin da biyu.
Binciken gidan jarida na Aljazeera da suke yi kowacce shekara dangane da tsawon awannin shan ruwa a ƙasashen duniya ya nuna cewa; A bana garin Nuuk na ƙasar Greenland shine inda suka fi awannin azumi kafin shan ruwa, sai sunyi awa 13 da mintuna 31 kafin su sha ruwa.
Rekyjavic na ƙasar Iceland shine gari na biyu da mutane ke yin azumin awanni 16 da mintuna 29 kafin su sha ruwa.
Hoton rahoton kasashen dake da awannin azumi masu tsayi.
Hoton rahoton kasashen dake da awannin azumi masu tsayi.
Binciken na Aljazeera ya nuna cewa a farkon azumin bana mutanen waɗannan ƙasashe basa wuce awanni 13 sannan su sha ruwa to amma lokacin yana ƙaruwa inda azumin ƙarshe zai kai awanni 16 da mintuna.
Hoton rahoton awanni azumi a kasashe.
Hoton rahoton awanni azumi a kasashe.

Sakamakon bincike:

Bisa samun bincike sahihi dangane da tsawon awannin azumin bana a ƙasashen duniya wanda ya bayyana cewa ƙasar Iceland bazata wuce awanni 16 da mintuna ba sannan su sha ruwa.
sannan kwana guda awanni ashirin da hudu ne kuma ikirarin na cewa sama da awanni ashirin da biyu wanda hakan ke nufin Shan ruwa da sahur baya wuce awa daya ko biyu kenan.
Wanna yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan iƙirari ƙarya ne.
Labarai Masu Alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da suka bayyana cewa ‘yan Najeriya sunyi asarar makudan kudade yayin...

Cirani: Shin Tarayyar Turai ta amince ‘yan Afrika su tsallaka ta Libya ba tare da Biza ba?

Duk da cewa kasashen turai na nuna damuwa tare da daukar matakan rage shigar bakin haure, ‘yan cirani dake...

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

  Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da...

Najeriya-Saudiyya sun karyata labarin cewa za’a hana ‘yan kasar bizar shiga Saudiyya

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta karyata ikirarin karya da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda ke cewa...

Karanta wannan

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar